Siyasar Kano: Bana shakkar Kwankwaso a takarar da muke yi –Shekarau
Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma dan takarar Sanatan mazaban Kano ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ko kadan baya shakkar fuskantar dan takarar Kwankwaso, Sani Aliyu Madakin Gini a takarar da suke yi.
Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 13 ga watan Feburairu yayin da yake zantawa da manema labaru a garin Kano game da zaben dake karatowa, inda yace jama’a ne zasu tabbatar da mai nasara a tsakaninsa da dan takarar Kwankwaso, Madakin Gini.
KU KARANTA: Atiku Abubakar ya bayyana muhimmin hakkin dake wuyan Buhari a 2019
“Dalilin shigata siyasa shine don na bauta ma jama’a ta hanyar sadaukar da kaina, don haka a matsayina na tsohon gwamna daya kwashe shekaru takwas bisa karagar mulki, ina da kyakkyawar fahimtar matsalolin da jama’ana ke fuskanta.
“Saboda haka bana jin tsoro ko shakka indai jama’a ne zasu zabi wanda suke so, ni kam naso ace da Kwankwaso zan fafata, domin kuwa a Kwankwaso Sanata ne dan bakara, bai taba taka kafarsa a Kano ba tun shekaru uku da rabi da suka gabata. Bai taba ganawa da al’ummar mazabarsa a cikin shekarun nan ba.” Inji shi.
Daga karshe tsohon gwamna Malam Shekarau ya bayyana tabbacinsa na samun nasara gagaruma akan abokin takararsa, Sani Aliyu Madakin Gini, wanda ya fito daga jam’iyyar PDP amma kuma darikar Kwankwasiyya.
Idan za’a tuna a kokarinsa na neman takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP ne Sanata Kwankwaso ya fasa tsayawa takarar komawa kan mukaminsa na Sanata, inda ya gwammaci ya nemi kujerar shugaban kasa, sai ya bar ma Madakin Gini ya takarar kujerarsa ta Sanata.
Kuma ko bayan da Atiku Abubakar ya lallasashi a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, Kwankwaso bai fasa janyewa daga takarar Sanatan ba, amma duk da wannan mataki daya dauka masana siyasar Kano na ganin idan Shekarau ya kayar da Madakin Gini, tamkar Kwankwaso ya kayar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng