Sarkin Musulmi Ya Yi Tir da Amurka Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza
- Mai alfarma Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi jawabi a game da munanan hare-haren da Israila ta ke kai wa mutanen Falasdinu
- Sultan ya fitar da jawabi ne ta bakin shugabannin majalisar NSCIA, ya na mai kira da ayi maza-maza a tsagaita wuta a kan zirin Gaza
- Shugaban jami’ar Al-Istiqamah, Farfesa Salisu Shehu da fitaccen lauyan nan, Ustaz Usman SAN su ka yi magana da yawun Sultan
Abuja - Majalisar NSCIA da ke karkashin Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ta yi Allah-wadai da yakin da ake yi a Gaza.
A rahoton Daily Trust, an ji cewa Mai alfarma Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III bai ji dadin yadda Amurka ta marawa Israila baya ba.
Jawabin da da aka samu a ranar Litinin ya nuna majalisar kolin musuluncin ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yankin na zirin Gaza.
Jawabin shugabannin NSCIA a kan Gaza
Mataimakin sakatare, Farfesa Salisu Shehu da Mai ba NSCIA shawara a kan shari’a, Yunus Ustaz Usman (SAN) ne su ka sa hannu a jawabin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin majalisar sun kira abin da ya ke faruwa da abin takaici a kan farar hula.
Rahoto ya ce NSCIA ta fito karara ta na sukar yadda gwamnatin Amurka ta ke goyon bayan kisan gillar da Israila ta ke yi wa Falasdinawa.
Sanarwar ta kara da cewa bai dace a rika kauda idanu daga neman zaman lafiya da yaki ya kaure tsakanin Falasdinawa da sojojin Israila ba.
Sultan ya na so Najeriya ta kare Falasdinawa
A karshen jawabin da Farfesa Shehu da Yunusa SAN su ka fitar, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta bada kariya ga wadanda ake zalunta.
Kamar yadda Najeriya ta goyi bayan bakake a lokacin yakinsu da fararen fata a Afrika ta Kudu, Sultan ya na so a mara baya ga Falasdinu.
Sultan ya zargi Israila da kisan kare dangi da gilla da neman ganin bayan marasa karfi bayan mummunan harin da sojojin Hamas su ka kai.
Fafaroma ya soki Israila
Ana da labari musulmai da ke karkashin kungiyar OIC za su yi zama a kan hare-haren da ake kai wa mutanen Falasdinu a zirin Gaza.
Sannan Fafaroma Franics ya yi suka saboda kisan gillar da ake yi na kwanaki.
Asali: Legit.ng