Sultan @65: Tarihi, nasaba, aikin soja, sarauta da yadda Sa'ad III ya zama Sarkin Musulmi na 20

Sultan @65: Tarihi, nasaba, aikin soja, sarauta da yadda Sa'ad III ya zama Sarkin Musulmi na 20

  • A yau 24 ga watan Agustan 2021 Sarkin Musulmi yake cika shekara 65
  • Muhammad Sa’ad Abubakar shi ne ‘dan auta wajen Sultan Abubakar III
  • Mahaifinsa ya shekara 50 kan kujerar Sarkin Musulmai, ya rasu a 1988

Sokoto - A ranar 24 ga watan Agusta irin ta yau a 1956 aka haifi Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III CFR, mni.

Hakan ya na nufin Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya cika shekara 65 a Duniya a yau Talata.

Legit.ng Hausa ta tsakuro kadan daga cikin tarihin Sultan domin masu bibiyar shafinmu su san rayuwar Mai alfarama Sarkin Musulman duk Najeriya.

Haihuwa

An dai haifi Sultan ne a ranar 24 ga watan Agusta, 1956 a garin Sokoto, jihar Sokoto. Shi ne ‘dan autan Sultan Abubakar III wanda ya rasu a karaga a 1988.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Sa'ad III ya cika shekara 65 a Duniya, Buhari ya aika masa sako na musamman

A lokacin da mahaifinsa ya rasu, Sa’ad III yana da shekaru kimanin 32, ya fara aiki a gidan soja. Bayan shekara 18 ya gaji sarautar da mahaifin ya mutu a kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A ina Sultan ya yi karatu?

Muhammad Sa’ad Abubakar ya shiga makarantar firamaren Sultan da ke garin Sokoto, daga nan ya samu shiga makarantar nan ta Barewa College, Zaria.

Karatu da tafiya Soja

Bayan kammala sakandare, Sultan ya samu zuwa makarantar koyon aikin soja na NDA da ke garin Kaduna, ya na cikin ‘yan aji na 18 da aka yaye a 1977.

Sa’ad Abubakar III ya kware a harkar yaki, ya jagoranci tawagar AU zuwa kasar Chadi. Ya yi aiki da ECOWAS a matakai dabam-dabam na tsawon shekaru.

Sarkin Musulmi ya yi aiki a Fakistan, Iran, Iraq, Afghanistan, Saudi Arabia a matsayin mai ba gwamnatin Najeriya shawara kan tsaro a kasashen wajen.

Kara karanta wannan

Hotunan bikin mika wa sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero sandar girma

A watan Disamban 2006 ne Mai alfarma ya bar Fakistan, ya ajiye aikin soja, ya na matsayin Birgediya-Janar, bayan an zabe shi a sabon Sarkin Musulmi.

Sarkin Musulmi na 20
Sultan na kasar Sokoto
Asali: UGC

Yaushe ya zama Sarkin Musulmi?

A Nuwamban shekarar 2006, Muhammad Sa’ad III ya zama Sarkin Musulmi bayan mutuwar ‘danuwansa, Ibrahim Muhammad Maccido a hadarin jirgin sama.

Mukamai

RFP ta ce Sultan, ne yake rike da kujerar shugaban majalisar kolin addinin musulunci na kasa, watau Nigeria Supreme Council for Islamic Affairs (NSCIA)

Haka zalika Muhammadu Sa’ad Abubakar III wanda shi ne Sarkin Musulmi na 20 a tarihi, shi ne shugaban kungiyar nan ta Jama’atu Nasril Islam da ke Kaduna.

Sarkin Musulmi da manyan addinin kiristanci su ne shugabannin majalisar NIREC mai kokarin kawo zaman lafiya da hadin-kai tsakanin addinai a Najeriya.

World Government Summit ta ce Sa’ad III ya na cikin ‘yan majalisar nan ta Religions for Peace.

Kara karanta wannan

Abun da ya kamata ku sani game da gimbiyar Kano wacce ta sace zuciyar ‘da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka

Yanzu haka Sultan ne shugaban jami’ar Ibadan, baya ga shugabancin majalisar sarakunan gargajiya. Shi ne babban mai sarautar gargajiya a fadin kasar nan.

Sa'ad III ya na da lambobin girma?

Mai alfarman ya samu lambar girma da digirin karrama wa daga jami’o’i kamar; Jami’ar Ahmadu Bello, UNIBEN, jami’ar Ibadan, jami’ar tarayya da ke garin Abuja.

Har ila yau jami’ar jihar Legas da ta jihar Anambra da jami’ar Usman Danfodio sun taba karrama shi.

Buhari ya fitar da jawabi

A ranar Litinin, mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi, yana yi wa Sultan fatan alherin kara shekara a ban kasa.

A jawabin da ya fitar, shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da aikin da Sarkin Musulmin na Najeriya ya yi a kusan shekaru 15 da ya shafe a kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel