NSCIA ta bukaci gwamnati ta dauki mataki a kan hudubar Igwebuike Onah
- Sarkin Musulmi ya soki hudubar Godfrey Igwebuike Onah da ta jawo kashe-kashe
- Majalisar NSCIA ta zargi Limamin da hura wutan rikicin da ya barke kwanan nan
- An kashe musulmai kuma an yi asarar dukiya kwanan a yankin kudancin Najeriya
Daily Trust ta rahoto cewa majalisar kolin addinin Musulunci ta yi kira ga gwamnatin tarayya da tayi maza ta dauki mataki a kan Godfrey Igwebuike Onah.
NSCIA ta yi wannan kira ne bayan hudubar Fasto Igwebuike Onah ta jawo an kashe wasu musulmai da ke zaune a kudu maso gabas da kudu maso kudu.
Majalisar musulman wanda Sarkin Musulmai ya ke jagoranta ta kai korafi gaban IGP, Mohammed Adamu da kuma shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi.
KU KARANTA: Shekau: Boko Haram sun fitar da sabon bidiyo
Taken da NSCIA ta yi wa takardun korafin shi ne: “Complaint on Rev. Father Godfrey Igwebuike Onah’s hateful sermon and its consequent murder of Muslims and destruction of their property in the south-east and south-south zones of Nigeria”
Mataimakin sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya na zargin wannan Faston da yin hudubar da ta jawo kashe musulmai tare da barnata dukiyoyinsu.
A takardun, Salisu Shehu ya sanar da shugaban ‘yan sandan Najeriya da DSS cewa an kai wa Musulmai hari babu gaira babu dalili a bangaren kudancin kasar.
“An kashe wasu an yi asarar dukiyarsu ta biliyoyi da aka sace, an barnata wasu ko kuma an banka masu wuta.”
KU KARANTA: Akwai rikici idan PDP ta hana Inyamuri tikitin Shugaban kasa a 2023
“An kona masallatai, daga ciki har da tsofaffin masallatan da asalin musulman Ibo su ka gina.” Inji Farfesa Shehu a madadin majalisar kolin addinin Musuluncin.
A cewar NSCIA, a maimakon lamarin ya lafa, abin kamari ya ke ta kara yi a wadannan yankuna.
Majalisar ta ce Godfrey Igwebuike Onah da wasu masu kiyayya ga musulunci sun yi huduba cike da karya a ranar 31 ga watan Oktoba, wanda ya jawo wannan asara.
Rahotanni sun ce sai da aka biya N8.5m kafin ‘yan bindiga su fito da wadannan Bayin Allah.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng