Kwara: 'Yan Bindiga Sun Fasa Gidan Dan Majalisa, Sun Sace Matarsa da 'Yayansa

Kwara: 'Yan Bindiga Sun Fasa Gidan Dan Majalisa, Sun Sace Matarsa da 'Yayansa

  • Yan bindiga sun yi garkuwa da mata ɗaya da 'ya'ya biyu na wani ɗan majalisar dokokin jihar Kwara da tsakar dare
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun kutsa cikin gida, suka tafi da su da misalin ƙarfe 1:00 na dare kuma har yanzu ba a gansu ba
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda ya tabbatar da lamarin amma ya ce bai samu cakakken bayani ba a yanzu

Jihar Kwara - 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mata da ‘ya’ya biyu na dan majalisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazaɓar Ipaiye/Malete/Olooru a karamar hukumar Moro.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa maharan sun kutsa cikin gidan ɗan majalisar da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar daren jiya wayewar garin ranar Talata, 17 ga watan Oktoba.

An sace mata da yayan ɗan majalisar dokokin Kwara.
'Ya'ya biyu da matar ɗan majalisa sun shiga hannun masu garkuwa a Kwara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wani shugaban al'umma a Shao ya ce:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'an Tsaron Haɗin Gwiwa Sun Yi Artabu da Makiyaya, Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu

"Masu garkuwan sun zo ne da yawa, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin daga bisani suka tasa ƙeyar wadanda abin ya shafa zuwa cikin dajin da ke kusa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Har yanzu ba a san inda suke ba duk da cewa daya daga cikin 'yan bindigan ya tuntubi ‘yan uwa amma har yanzu bai nemi kudin fansa ba. Ya ce ba ya tare da sauran a dajin shiyasa ba su faɗi kuɗin da za a basu ba."
"Amma a halin da ake ciki yanzu an shawarci ɗan majalisar ya tashi daga garin ya koma wani wuri daban."

Yayin da aka tuntuɓi ɗan majalisar da wayar salula don jin ta bakinsa bai ɗaga kiran ba.

Wane mataki aka ɗauka kawo yanzu?

Amma shugaban ‘yan banga na jihar, Alhaji Ibrahim Saka, ya ce, “Eh gaskiya ne kuma mun tura da wasu daga cikin mutanen mu domin su tsefe dajin su ceto su."

Kara karanta wannan

Gwammatin Tinubu Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Mutane Aikin N-Power Na 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Vanguard ta rahoto kakakin 'yan sandan na cewa:

"Har yanzun ba bu cikakkun bayanai a ƙasa amma da zaran mun samu bayani zamu dawo gare ku," in ji shi.

Kano: Yan Sanda Sun Kama Mutum 30 Kan Yunkurin ‘Tayar Da Tarzoma’ Yayin Auren Gata

A wani rahoton na daban Yan sanda sun cafke mutane 30 da ake zargin suna yunƙurin kawo cikas a bikin Auren gata da aka yi ranar Jumu'a a Kano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Gumel, ya ce mutanen sun bayyana abin da ya kawo su wurin ɗaura aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel