Abdussamad Rabiu Ya Ci Ribar Fiye da Naira Biliyan 1 a Cikin Sa’o’i 24 Kacal
- Abdussamad Rabiu wanda shi ne na biyu a masu arzikin Najeriya ya samu ribar fiye da Naira biliyan daya a cikin sa’o’i 24 kacal
- Wannan kazamar riba da ya samu ta kara zaunar da shi a matakin da ya ke na masu arzikin Nahiyar Afirka wanda ya ke mataki na shida
- Alhaji Aliko Dangote shi ke jagorantar teburin masu kudin Nahiyar Afirka yayin da dan Afirka ta Kudu Rupert Johann ke biye masa a mataki na biyu
Mamallakin kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu ya samu riba a cikin sa’o’i 24 kacal a wannan mako da mu ke ciki.
Rahoton Bloomberg ta ruwaito cewa attajirin ya samu ribar Naira biliyan 1.5 a sa’o’i 24 kacal inda a yanzu ya ke da kudi Dala 5.98.
Ribar nawa Abdussamad Rabiu ya samu?
Wannan ribar da ya samu ya tabbatar da shi a cikin masu arzikin Nahiyar Afirka wanda kuma ya dawo na 403 a duniya, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mafi yawan arzikin Rabiu na zuwa ne daga kamfanin siminti na BUA wanda shi ne kamfani na biyu a Najeriya da ya ke fitar da siminti.
Rabiu na da hannun jari a kamfanin fiye da kashi 95 na dukkan hannun jari da ke kamfanin da kuma wasu wurare.
Wane karuwa Abdussamad Rabiu ke samu?
Tun bayan rage farashin siminti daga dubu 5 zuwa 3,500 kamfanin ya kara samun karin farashin hannun jari daga Naira 94 a ranar 6 ga watan Oktoba zuwa Naira zuwa Naira 105 a ranar 16 ga watan Oktoba.
Har ila yau, hannun jarin Rabiu na kamfanin siminti na BUA Naira biliyan 32.5 ya karu daga Naira tiriliyan 3.4 zuwa Naira tiriliyan 3.41 a cikin kwanaki 10 kacal.
Jerin masu kudin Nahiyar Afirka:
1 Aliko Dangote Dala 16.3bn
2 Johann Rupert Dala 10.7bn
3 Nicky Oppenheimer Dala 8.88bn
4 Natie Kirsh Dala 7.10bn
5 Nassef Sawiris Dala 7.49bn
6 Abdulsamad Rabiu Dala 5.98bn
7 Naguib Sawiris Dala 5.59bn
Kamfanin BUA ya rage farashin siminti
A wani labarin, kamfanin siminti na BUA ya rage farashin kaya zuwa 3,500 a Najeriya.
Kamfanin ya sanar da cewa dokar za ta fara aiki a ranar 2 ga watan Oktoban wannan shekara da mu ke ciki.
Asali: Legit.ng