Kotu Ta Yankewa Masu Asirin Kudi 5 Hukuncin Shekaru 12 a Gidan Yari, Ta Saki Boka

Kotu Ta Yankewa Masu Asirin Kudi 5 Hukuncin Shekaru 12 a Gidan Yari, Ta Saki Boka

  • An kama wasu gawurtattun masu asirin kudi biyar tare da hukunta su a yankin arewa maso tsakiya
  • Rahoto ya nuna an kama wadannan mutane ne da kan wani mutum da aka tono daga wata makabarta shekaru uku bayan binne shi
  • An tattaro cewa lamarin ya afku ne a watan Satumba, kuma kotu ta saki bokan da ya kamata a kai wa kan don yin asirin kudin

Minna, Niger - Wata kotu a Minna, jihar Neja, ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin shekaru 12 a gidan yari kan tono kan wani mutum daga makabarta.

An tattaro cewa sun yi niyan kai a wani boka da ya bukaci su kawo kan don yi masu asirin kudi ne.

An garkame wasu mutane da aka samu da kan mutum
Kotu Ta Yankewa Masu Asirin Kudi 5 Hukuncin Shekaru 12 a Gidan Yari, Ta Saki Boka Hoto: PIUS UTOMI EKPEI
Asali: Getty Images

Mazajen sun fallasa abun da suka aikata ne bayan an kama su dauke da kan mutum din.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Sanda Suka Kama Fasto da Wasu Mutum 3 da Kokon Kan Dan Adam, Sun Fadi Abin da Za Su Yi da Shi

Yadda aka kama matasa da kokon kan mutum

A cewar mai gabatar da karar, sun tono gawar wani mutum da aka binne ne shekaru uku da suka gabata a makabartar musulmai da ke jihar Neja, a arewa maso tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda sashin BBC ya rahoto, mai gabatar da karan ya ce:

"Sun ce bokan ya sanar da su sannan ya yi wa dukkansu alkawarin cewa za su raba kudin da suka samu a ta'asar sannan ya umurce su da su je su nemo kan mutum."

Jami'an tsaro ne suka kama wadannan munate, masu shekaru tsakanin 18 da 28 a farkon watan Satumba yayin da suke shirin kai kan ga bangare na uku, bisa umurnin bokan.

Kotun ta same su da laifin hada baki, da keta haddin makabarta, da kuma mallakar kokon kan mutum ba bisa ka’ida ba. Sannan ba a kama bokan ba kuma ba a tuhume shi ba.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yanayi Bayan ’Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas a Jihar Arewa, Mutum 1 Ya Mutu, An Raunata 2

Matashi ya firgita da ganin wata halitta kusa da janaretonsa

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya kan wata halitta da ya gani a gefen janaretonsa.

Da ya garzaya shafinsa na TikTok, mutumin mai suna @timitrey, ya yada bidiyon halittar, cewa yana shirin kunna janaretonsa ne ya ci karo da ita.

Matashin ya ce ya tsorata matuka sannan ya nemi a kawo masa agaji. A wani bidiyo da ya biyo baya, wani mai karfin hali ya bayyana a wajen sannan ya taimaka wajen korar halittar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel