Tinubu Ya Yi Bindiga da Naira Miliyan 400 Wajen Kama Otel a Taron UN a Amurka

Tinubu Ya Yi Bindiga da Naira Miliyan 400 Wajen Kama Otel a Taron UN a Amurka

  • Bola Ahmed Tinubu ya na cikin shugabannin Duniya da aka gayyata wajen babban taron majalisar dinkin duniya a birnin New York
  • Tawagar shugaban Najeriyan ta kashe makudan daloli a zaman da ta yi na tsawon mako guda a wani katafaren otel da ke kasar Amurkan
  • Takardar da aka samu ta nuna kama dakuna sun ci $507,384, idan aka yi lissafi a farashin ‘yan canji, kudin nan sun kai Naira rabin Biliyan

Abuja - Kudin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kashe a wajen halartar taron majalisar dinkin duniya kwanaki ya jawo surutu a gida.

Binciken jaridar FIJ ya nuna gwamnatin tarayya ta batar da $507,384 domin tawagar shugaban kasa ta kama dakuna kurum a dankareren otel.

Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya na cikin wadanda su ka je babban taron da majalisar dinkin duniya ta shirya a New York a Amurka.

Kara karanta wannan

Dalla Dalla: Yadda Najeriya Ta Ke Shirin Kashe Naira Tiriliyan 26 a Shekarar 2024

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya a UN Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya tare a St. Regis Hotel

Wata takarda da aka bankado ta nuna yadda aka kashe $422,820 domin a biya kudin dakunan da za a zauna a birnin na New York a Satumba

Tawagar shugaban Najeriyan ta zauna ne a wani otel mai suna St. Regis Hotel.

A lissafin da aka yi, otel din sun karbi N325.5m a matsayin kudin kwana, sai kuma wasu ragowar Dala $84,564 (wanda ya haura N65.1m).

Gwamnatin Najeriya ta biya karin kusan 20% ne saboda abin da zai iya kai ya komo a otel din, wasu su na ganin kudin sun yi matukar yawa.

Tinubu ya yi kwana 7 a otel

Shugaba Tinubu da ‘yan rakiyarsa sun zauna a otel din na St. Regis Hotel mai dan karen tsada ne daga 16 zuwa 23 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Nemi Cin Sabon Bashin Dala Miliyan 400 Daga Bankin Duniya

Takardar da aka samu ba ta iya yin cikakken bayanin yadda aka kasa miliyoyin kudin ba. Tashar Arise ta tabbatar da rahoton nan a jiya.

Daga ina kudin su ka fito?

Babban sakataren gwamnati a fadar shugaban kasar, Adebiyi O. Olufunso ya sa hannu a takardar domin a biya wadannan makudan kudi.

Kamar yadda umarnin ya nuna, an sanar da ma’aikatar kudi da ofishin Akanta Janar su biya dalolin da zarar shugaban kasa ya rattaba hannu.

An bukaci a fitar da kudin daga wani asusu da aka bude domin samar da isasshen abinci.

Kun ji labari Najeriya na tunanin yin kasafin da ba a taba ganin irinsa ba. Kasafi mafi tsada da aka yi shi ne N21tr a lokacin Muhammadu Buhari.

A shekarar farko a ofis, Bola Ahmed Tinubu ya na harin batar da abin da ya zarce N26tr. Fiye da 30% za su tafi ne a wajen biyan tsohon bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel