“Bai Yi Ilimin Boko Ba”: An Karamma Dattijon Da Ya Kirkira Janareto Mara Amfani Da Mai Da Digiri
- Injiniya Hadi Usman, an karrama dan Najeriya da ke kirkiran abubuwa ba tare da ilimin boko ba da digirgir
- Dattijon mai shekaru 70 ya kera janareto mara amfani da mai, risho da ken aiki da ruwa da kuma jirgi mai saukar ungulu mai injin din Vespa
- Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjinawa mutumin mai cike da baiwa, inda wasu suka yi kira ga masu hannu da shuni da su mayar da hankali a kansa
Jihar Gombe - Jami'ar jihar Gombe ta karrama dan Najeriya mai kirkiran abubuwa, Injiniya Hadi Usman da digirgir a bangaren kimiyya.
A cewar babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara ta musamman kan harkokin labarai, Safianu Danladi Mairiga a dandalin X, an bai wa Usman shaidar digiri a bikin yaye dalibai na jami'ar jihar Gombe da aka kammala kwanan nan.
Legit Hausa ta rahoto cewa Usman ya kirkiri risho mai amfani da ruwa. Sauran abubuwan da mutumin mai tarin baiwa ya kirkira sun hada da gidan radiyo, jirgi mai saukar ungulu wanda ke aiki da injin din Vespa da wayar hannu.
Danladi ya bayyana cewa Usman ya kuma kera wani janareto wanda baya aiki da fetur amma kuma bai yi ilimin boko ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewar mutumin haifaffen gudunmar Jekadafari da ke karamar hukumar Goimbe, jihar Gombe ya haddace Al-Qur'ani mai girma tun yana da shekaru 12 a duniya.
Danladi ya yada hoton Usman a zaune yayin da yake sanye da kayan karramarsa.
Kalli wallafar Safiyanu a kasa:
Jama'a sun yaba ma Hadi Usman
@YusufNasir_Ahmd ya ce:
"Magana ta gaskiya, wannan janareton mai amfani da ruwa da risho mai amfani da ruwa ba zai taba shiga kasuwa ba.
Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya
"Ilimin makamashi da aka kirkira a kyauta ba zai taba kaiwa kasuwa ba."
@Dammyjah2040 ta ce:
"Kun san me baya bayyana tsaraici....Babban kamfani ba zai zuba jari a kansa ba."
@papaanache ya ce:
"Me ya sa manyan yan Najeriya ba su yi amfani da damar wannan mutumin ba? Ba ma daraja hazaka a Najeriya kuma abin ya munana sosai. Ba ma maganar gwamnati bace, hatta masu hannu da shuni za su iya saka hannun jari a wannan baiwa na hakika. Abu ne da karara ya nuna za a samu riba kuma zai daga darajar Najeriya."
@MahmoodSalisu ya ce:
"Da dan tallafi kadan, mutane kamar su mallam Hadi za su yi abun al'ajabi sannan su zamo madubin duba ga mutane da dama don su yi koyi da shi. Amma a;a, mun gwammaci mu dunga sace kudin jama'a da kera gidaje a Dubai."
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu kan wannan dattijon:
Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki
Wata lakcara a Jami'ar jihar, Malama Hafsa Mohammed D. ta ce a gaskiya wanna karrawawa da aka yi wa dattijon abin a yaba ne ganin irin gudummawar da ya bayar.
Ta ce:
"Irin wadannan mutane su ka cancanci karramawa a Jami'o'i musamman na digirin digirgir ba wasu 'yan siyasa ba."
Yayin da Malami a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Kashere, Abubakar Anas ya ce:
"Na yi matukar farin ciki da irin karramawar, hasalima tun ba yau ba na ke muradin ganin an inganta harkokin wannan dattijo."
Dalibi a Jami'ar jiha, Aliyu Abubakar Yusuf ya ce farin ciki ya kusa saka shi kwalla saboda yadda ya ki dattijon ya burge shi.
Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Bi Titi Tana Rokon a Hada Mata Kudin Siyan iPhone 15 Ya Ba da Mamaki
A wani labarin, wata kyakkyawar mata ‘yar Najeriya ta bai wa mutane da dama mamaki lokacin da ta dauki kwali da ke dauke da kalmonin rokon kudin siyan waya iPhone 15.
Mutane da yawa da suka ganta a titi tana neman kudin da za ta sayi waya iPhone 15 sun yi mamaki kuma ba su boye yadda suka ji game da matakin nata ba.
Asali: Legit.ng