Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30

Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30

  • Idan ana maganar fasaha, Allah ya yiwa yan Najeriya baiwa kuma suna amfani da shi wajen kera ababen hawa na cikin gida
  • Shahararren injiniyan nan mai kera motoci a Maiduguri, Mustapha Gajibo ya fara sakin adaidaita sahu masu amfani da lantarki ga jama’ar gari
  • Hoton aikin da yayi na baya-bayan nan ya burge yan Najeriya a soshiyal midiya kuma sun nemi gwamnati ta tallafa masa don ya yi wasu da yawa

Borno - Kyawawan hotunan adaidaita sahu masu aiki da lantarki wanda kamfanin Phoenix Renewable Limited ya kera a Maiduguri sun yadu a shafukan soshiyal midiya.

Hadaddun hotunan adaidaita sahun wanda ake yiwa lakabi da Keke Napep ya sanya yan Najeriya da dama tofa albarkacin bakunansu sannan sun bukaci gwamnati da ta tallafawa kamfanin.

Kara karanta wannan

Wani Mai Adaidaita Ya Yiwa Kekensa Kwaskwarima Harda Kofofin Gilashi A Jos, Abun Ya Burge Mutane

Shugaban kamfanin da ya kera adaidaita sahun, Mustapha Gajibo ya shahara wajen yin ababen hawa masu aiki da lantarki wanda yawancinsu motocin bas-bas ne.

Adaidaita sahu da Gajibo
Hotuna: Dan Maiduguri Ya Kera Adaidaita Mai Aiki Da Lantarki Wanda Ka Iya Gudun 120Km Bayan Chajin Minti 30 Hoto: Northeast Reporters
Asali: Facebook

An tattaro cewa sabon keken adaidaita sahun zai iya tafiyar kilomita 120 bayan an chaja shi na tsawon mintu 30.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masu amfani da Facebook sun yi martani

Yan Najeriya da dama sun je sashin sharhi na wallafar da Northeast Reeporteers ta yi a Facebook don bayyana ra’ayoyinsu. Kalli wasu daga cikin martanin a kasa:

Akpama Obeten Enang ya ce:

“Wanene yace Najeriya ba za ta zama kasar da za a yi kishi da it aba idan muka yarda muka binne son zuciyar da ya raba mu sannan muka rungumi wadanda suka hada mu da zuciya daya.”

AbdulGaneey Baba Ajia ya yi martani:

“Alamar nasara saboda duk bayan yaki inda jihar tayi nasara, sai sauyi mai amfani ya biyo baya. Borno jihata mai albarka tana tasowa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yan Najeriya Sun Hadawa Matashin Da Ya Yi Shekaru 12 A Kurkuku Kudi Don Ya Fara Sana’ar Wanki Da Guga

Augustine Sylvester ya ce:

“Allah zai ci gaba da bunkasa iliminka idan manyan mutane da ke Maiduguri suka ki tallafa maka don ka bunkasa ba za su iya hana Allah bunkasa ka ba.”

Abdullahi Ibrahim ya ce:

“Wannan ne labaran da ya kamata su dunga fitowa daga arewa. Ba garkuwa da mutane, Boko Haram, fataucin yara da sauran laifuka ba. Matasan arewa. Ku tashi ku sauya labarin.”

Mustapha Gajibo Ya Kera Motocin Bas Masu Amfani Da Lantarki, Hotunan Sun Kayatar Da Mutane

A gefe guda, mun ji cewa yan Najeriya a soshiyal midiya sun cika da murnar ganin sabbin motocin bas masu amfani da lantarki wanda Injiniya Mustapha Gajibo ya kera a Maiduguri.

Gajibo wanda ya kasance sanannen injiniyan makamashi ya wallafa kayatattun hotunan sabbin motocin bas din a shafinsa na Twitter wanda ya burge mutane da dama.

An tattaro cewa sabbin motocin bas din mai cin mutum 12 zai iya gudun kilomita 212 bayan chaji daya tare da shafe tsawon kilomita 110 duk awa daya.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Kyakkyawar Diyar Sarkin Kano, Ruqayya Bayero Da Angonta Amir Kibiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel