Fusatattun Matasa Sun Yi Wa Sifetan Dan Sanda Kisan Gilla a Jihar Delta

Fusatattun Matasa Sun Yi Wa Sifetan Dan Sanda Kisan Gilla a Jihar Delta

  • Abin tausayi ya afku a jihar Delta bayan wasu matasa sun yi wa wani sifetan ‘yan sanda kisan gilla a jihar
  • Marigayin mai suna Festus Onori ya rasa ransa ne a jiya Lahadi yayin da ya ke tafiya zuwa coci don yin bauta
  • Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Bright Edafe ya ci tura saboda bai amsa kiran waya da aka yi ba

Jihar Delta – Wasu fusatattun matasa sun hallaka wani sifetan ‘yan sanda a yankin Pgwashi-Uku a karamar hukumar Aniocha ta Kudu da ke jihar Delta.

Marigayin mai suna Festus Onori ya rasa ransa ne a hannun matasan wadanda ma su sana’ar achaba ne a jihar.

Matasa sun yi ajalin wani sifetan dan sanda a jihar Delta
Fusatattun Matasa Sun Yi Ajalin Sifetan Dan Sanda a Delta. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Yaushe aka yi ajalin dan sandan a Delta?

Daily Trust ta tattaro cewa dan sandan ya yi aiki a ofishin rundunar da ke Marine inda aka mishi kisan gilla a gaban matarsa da ‘ya’yansa uku.

Kara karanta wannan

Gaza: Saudiyya Ta Kira Taron Musulmai, Fafaroma Ya Tsawata Wa Isra'ila

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi 15 ga watan Oktoba yayin da su ke tafiya zuwa coci don yin ibada.

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Bright Edafe bai samu ba yayin da bai daga kiran waya da aka mishi ba da amsa sakwannin da aka tura mishi a waya.

Sai dai wani dan uwan marigayin mai suna Austin Onori ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan dan wani achaba ya bugi bayan motar marigayin.

Wane martani dan uwan dan sandan ya yi?

Ya ce dalilin hakan ya sa dan uwan nasa fito wa don duba irin barnan da ta afku tare da duba lafiyar mai babur din, Thestoryng ta tattaro.

Austin ya kara da cewa kafin dan uwan nasa ya Ankara sai ga matasa fiye da 20 sun nufo shi da makamai inda su ka rufa ma sa.

Kara karanta wannan

Ana Cikin Yanayi Bayan ’Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Bas a Jihar Arewa, Mutum 1 Ya Mutu, An Raunata 2

Ya ce:

“Matasan sun ci gaba da binshi bayan tafiya mai tsawo inda mai din motarsa ya kare, su ka far ma sa kusan su 200 a tare da ajalinshi a gaban matarsa da ‘ya’yansa.
“Matasan sun kuma lalata ma sa motarsa inda ya ce yanzu haka gawarshi na dakin ajiyar gawarwaki a asibiti.”

'Yan sanda sun cafke Fasto da kokon kan dan Adam

A wani labarin, 'yan sanda sun kama wani Fasto da kokon kan dan Adam a jihar Ogun.

Rundunar ta kama Faston ne da wasu mutane uku da su ke tsafi da kayan don samun kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.