BBC Ta Tsaya Kan Bakanta Cewa Tinubu Bai Kirkiri Jabun Satifiket Ba

BBC Ta Tsaya Kan Bakanta Cewa Tinubu Bai Kirkiri Jabun Satifiket Ba

  • Tawagar tantance bayanai na BBC sun tsaya kan rahotonsu na cewa Shugaba Bola Tinubu bai ƙirƙiri takardar karatunsa ta jami'ar jihar Chicago (CSU) ba
  • Sashen ƙorafe-ƙorafe na kafar yada labaran ya ce bai ji daɗin yadda wasu mutane ba su ji daɗin binciken da suka yi kan takardar shaidar karatun Tinubu ba
  • BBC ta ce CSU ta tabbatar da cewa Tinubu ya kammala karatunsa na jami'ar kuma babu wata shaida cewa ya yi jabun satifiket

London, Ingila - Kamfanin yada labarai na Birtaniya (BBC) ya dage cewa babu wata shaida da ke nuna cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jabun takardar shaidar kammala karatunsa a jami'ar jihar Chicago (CSU).

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun sashen ƙorafe-ƙorafe na BBC da ta aikewa masu sauraronta a ƙarshen mako, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Daidaita Digiri da HND a Najeriya? Hukumar NUC Ta Bayyana Gaskiya

BBC ta sake magana kan takardun Tinubu
BBC ta ce har yanzu ba wata shaida cewa Tinubu ya yi satifiket na bogi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Kafar yada labaran ta ce ta tsaya daram kan binciken ta duk da ƙorafe-ƙorafen da wasu mutane suka aike mata.

BBC ta nuna takaicin cewa wasu mutane ba su ji daɗin "binciken da muka yi kan wannan batu ba".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar na cewa:

"Mun samu irin waɗannan ƙorafe-ƙorafe da dama kuma mun yi nadamar cewa ba ku ji dadin binciken da muka yi kan wannan batu ba. Mun bincika kuma BBC ba ta ga wata shaida da ke nuna cewa satifiket ɗin na bogi ne."
"Mun tuntubi jami'ar jihar Chicago kuma sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya kammala karatunsa a jami’ar a shekarar 1979 da digirin farko. Mun yi amanna cewa rubutun mu ya kasance mai ba da bayani na gaskiya da aka sani. Domin haka muna goyon bayan aikin da muka yi.

Kara karanta wannan

Ministan Birnin Tarayya Nyesom Wike Ya Bayyana Dalilin da Yasa Ya Yarda Ya Yi Aiki da Tinubu

Shugaba Tinubi Ya Aike da Bukata Ga Kotun Koli

A wani labarin na daban kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci kotun ƙoli da kada ta karɓi sabbin hujjojin da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar mata.

Shugaban ƙasar ya bayar da dalilin cewa lokaci ya wuce da kotun za ta karɓi sabbin hujjoji a shari'ar da suke yi kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel