Auren Gata: Kwankwaso Ya Fadawa Ma’aurata Sirrin Yadda Za Su Zauna Lafiya

Auren Gata: Kwankwaso Ya Fadawa Ma’aurata Sirrin Yadda Za Su Zauna Lafiya

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jawabi a wajen walimar aurar da angwaye da amare sama da 1, 500 da aka yi a jihar Kano
  • Tsohon Gwamnan ya yi kira ga wadanda aka aurar su guji laluben wayoyin junansu idan har su na so aurensu ya yi karko
  • A zamanin nan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce babu abin da ya ke yawan raba aure a duniyar yau irin duba wayoyi

Kano - Rabiu Musa Kwankwaso wanda jagora ne a jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ya halarci walimar auren gata da aka shirya.

Gwamnatin jihar Kano ta aurar da maza da mata 1, 800, Daily Trust ta rahoto abin da ya wakana wajen walimar auren da aka yi a yau.

An gudanar da walimar ne a gidan gwamnati, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa ma’uratan hudubar yadda za su zauna lafiya.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Tsallake Rijiya da Baya Yayin da Aka Kai Masa Harin Kisa Sau 4 a Arewa

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Kwankwaso ya ce a guji duba wayar salula

Tsohon gwamnan ya ja-kunnensu a game da duba wayoyin mazajensu, yake cewa laluben salulan ya na yawan kashe aure a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya bada shawara ga sababbin auren su guji abin da zai iya kawo matsala.

An ba ku shawarwari daga kowane bangare. Na yi imani an ba ku shawarwari sosai.
Malamai, iyaye, ‘yanwa har da ‘yan kasuwa sun ba ku shawarar yadda za ku zauna cikin zaman lafiya da junanku.
Amma ina da shawara guda a gare ku; ita ce duba wayoyin abokan zamanku. Ka da ku rika leka wayoyin juna.
Hakan shi ne babban abin da ya ke raba aure a zamanin nan."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir Yusuf

Vanguard ta ce Madugun na Kwankwasiyya ya jinjinawa Abba Kabir Yusuf a kan yadda ya dawo da tsarin aurar da marasa karfi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Shiga Makoki Bayan Rasuwar Fitaccen Dan Siyasa Bello Maitama a Kano

Kwankwaso ya yabi yadda gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf za ta kashe N700m wajen daukar dawainiyar yara 600 a kasashen waje.

Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya

Kamar yadda aka ji labari, Aminu Sani Jaji wanda ya san harkar tsaro ya yi tir da rashin jituwa tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya.

‘Dan siyasar ya ce da gwamnati za ta dage, lamarin satar mutane zai kare, yake cewa matsalar za ta iya nakasa sha’anin ilmi a Arewacin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng