Yadda Wata Kyakyawar Mata Ta Auri Kanta Da Kanta Bayan Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudin Aurenta

Yadda Wata Kyakyawar Mata Ta Auri Kanta Da Kanta Bayan Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudin Aurenta

  • Wata mata mai suna Sarah Wilkinson ta cika burinta na yin irin shagalin da take muradi a ranar aurenta
  • Matar ta auri kanta da kanta bayan ta shafe tsawon shekaru 20 tana tara kudin da za ta yi irin wannan biki
  • Shagalin bikin wanda aka yi a Felixstowe, Suffolk, ya samu halartan yan uwa da abokan arziki, inda aka girgije

Wata mata da ta shafe tsawon shekaru 20 tana tara kudi don yin kasaitaccen biki da take mafarki ta auri kanta da kanta bayan ta gaza samun abokin rayuwa da ya dace da ita.

Sarah Wilkinson, mai shekaru 42 a duniya ta yanke shawarar yin shagalin biki wanda shahararriyar aminiyarta ta gudanar a Harvest House da ke Felixstowe, Suffolk, rahoton BBC.

Wata mata ta auri kanta da kanta
Yadda Wata Kyakyawar Mata Ta Auri Kanta Da Kanta Bayan Ta Shafe Shekaru 20 Tana Tara Kudin Aurenta Hoto: BBC.com
Asali: UGC

"Yadda na shafe tsawon shekaru 20 ina tara kudin aurena", matar da ta auri kanta

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Fusata Ta Juye Ruwa a Gadonsu Na Sunna Saboda Miji Ya Ki Siya Mata Gashin Kanti

Matar ta ce ta yanke shawarar yin shagalin ne bayan ta siyawa kanta zoben alkawari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya kasance ranar farin ciki a gareni ganin yadda hankali ya koma kaina."
"Bikin ba na aure a hukumance bane, amma dai na yi bikin aurena.
"Ina ganin zai kai gabar da za ka yi tunani 'ba lallai ne na yi wannan tare da abokin rayuwata a gefena ba, amma mai zai sa na rasa wannan damar?'
"Wannan kudin na kebe shi don aurena ne - magana ce ake na ga shi nan kuma mai zai sa ba zan yi amfani da shi a kan abun da nake son yi ba."

Ms Wilkinson, wacce ke zama a cikin gari, ta ce ta kashe £10,000 kan bikin bayan tana ware kudi duk wata da kuma kara duk wata rarar kudi da ta samu.

Kara karanta wannan

Masanan Duniya Sun Taimaki Tinubu da Muhimman Shawarwari da $1 ta Zarce N1000

Matar ta kasance kewaye da yan uwa makusanta da abokanta 40 a wajen bikin da aka yi a ranar 30 ga watan Satumba sannan tare da wasu mutum 40 a yammaci a wajen buga wasar kwallon tebur.

Ta fada ma sashin BBC Radio Suffolk cewa kawayenta ba su yi mamaki da jin shirinta na auren kanta ba.

"Babu wanda ya daina murmushi tsawon ranar kuma kowa cewa yake wannan irin lokaci na ban al'ajabi da suka shafe," inji ta.

Ban cire tsammanin samun ango a nan gaba ba, Ms Wilkinson

Ms Wilkinson ta ce ta rubuta alkawara 14 da za ta karmama, wanda na farkon shine alkawarin ba za ta daina sarrafa rimot din talbijin ba.

Ta ce ta yanke shawarar yin aure ne lokacin da ta cika shekaru 40 sannan ta siyawa kanta zoben alkawari na lu'u-lu'u wanda take matukar so.

Kawarta wacce ta shahara wajen tsara bukukuwa, Katherine Cresswell ce ta shirya bikin.

Kara karanta wannan

An Kori Ma’aikaciya Daga Wurin Aiki Bayan Gano Ta Kwanta da Maza Sama da 300

Sai dai kuma, duk da yin bikin aurenta, Ms Wilkinson bata cire tsammani ba na haduwa da angonta a nan gaba.

Wata tsaleliyar budurwa yar kasar Indiya za ta auri kanta, an kammala tsara biki

A wani labari makamancin wannan, wata mata mai suna Miss Kshamu Bindu, akasar Indiya ta shirya auren kanta a wani biki na gargajiya da za a yi a ranar 11 ga watan Yunin 2022.

Ta kasance sanye da kayan amare, da lalle na zamania hannunta da hoda a kanta, amaryar za ta yi zagaye wuta sau bakwai kamar yadda aka saba a auren al'adarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng