Dalilin Dauko Ola Olukoyede, Na Ba Shi Shugabancin EFCC Inji Bola Tinubu

Dalilin Dauko Ola Olukoyede, Na Ba Shi Shugabancin EFCC Inji Bola Tinubu

  • Nadin sabon shugaban hukumar EFCC ya jawo surutu da zargin shugaban Najeriya da sabawa kundin tsarin mulkin kasa
  • Bola Ahmed Tinubu a jawabin da ya fitar a dandalin X, ya kafe da cewa Olu Olukoyede ya cancanci ya jagoranci EFCC a doka
  • Jawabin ya fito ta bakin Mr. Fredrick Nwabufo inda karyata masu ikirarin nadin ya ci karo da dokar da ta kafa hukuma a 2004

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi magana a kan abin da ya sa ya nada Olu Olukoyede domin ya jagoranci hukumar EFCC.

Wasu masana sun fito su na zargin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da saba doka, su ka ce sam Olu Olukoyede bai cancanci kujerar ba.

A martanin da ya maida ta bakin mai taimaka masa, Fredrick Nwabufo, shugaban Najeriyan ya tabbatar da dacewar lauyan a EFCC.

Kara karanta wannan

An Saba Doka Wajen Nadin Sabon Shugaban EFCC - Tsohon Jigon APC

Ola Olukoyede
Sabon shugaban EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @PIDOMNIGERIA
Asali: Twitter

Olu Olukoyede ya dace ya rike EFCC

Jawabin Mista Fredrick Nwabufo a X zai iya zama raddi ga wadanda ke ikirarin saba doka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin ya ce nadin bai ci karo da sashe na 2(3) dokar da ta kafa hukumar EFCC a 2004 ba domin an yi aiki da kundin tsarin mulki.

EFCC: Hujjar da Fredrick Nwabufo ya kawo

"Mista Olukoyede shi ne shugaban ma’aikatan shugaban EFCC (2016-2018) kuma Sakatare na hukumar (2018-2020).
Ya na cikin hukumar tabbatar da shari’a a matsayin sakatare, a na shi halin, a EFCC, kamar yadda doka ta tanada.
Saboda haka ya cika duk wasu sharuda a doka na zama shugaban hukumar.
Sannan sashe na 2(1)(p) na dokar EFCC ta fada karara, a fayyace cewa sakataren hukumar (EFCC) ‘dan ta ne kuma shi ne shugaban gudanarwa."

- Fredrick Nwabufo

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar EFCC Wanda Ya Maye Gurbin Bawa

Hadimin shugaban kasar ya ce kotun koli a shari’ar Ejuetami v. Olaiya & Anor (2001) LPELR-1072 (SC) ta raba wannan gardama tuni.

Leadership ta ce a cikin hujjojin fadar shugaban kasa shi ne babu inda doka ta takaita aikin da ake bukatar shugaban ya yi na shekaru 15.

A cewar Fredrick Nwabufo, ba dole ba ne sai wanda zai rike EFCC ya yi shekaru 15 ya na aikin shari’a ko damara, don haka an bi dokar kasa.

Lauyoyi 58 sun zama SAN

Ku na da labari an yi waje da Farfesoshi sama da 10 daga jami’o’i a cikin lauyoyi 58 da za su zama SAN kamar yadda LPPC ta saba a shekara.

Olukayode Ajulo, Felix Offia, Lawrence Falade, Kingsley Obamogie, Folasade Alli sun shiga jerin wadanda su ka zama manyan lauyoyin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng