‘Dan Majalisar APC Ya Fadi Abin da ke Hana a Kawo Zaman Lafiya a Jihohin Arewa

‘Dan Majalisar APC Ya Fadi Abin da ke Hana a Kawo Zaman Lafiya a Jihohin Arewa

  • Aminu Sani Jaji ya soki gwamnatoci a kan yadda su ka gagara kawo zaman lafiya musamman a jihohin da ke yankin Arewa
  • ‘Dan majalisar Birnin-Magaji/Kauran Namoda ya zargi gwamnati da rashin ganin dama, yake cewa za a iya yakar ‘yan bindiga
  • Hon. Jaji ya taba shugabantar kwamitin tsaro a majalisar tarayya, ya soki sulhu da ake yunkurin yi da ‘yan ta’ddan kasar

Abuja - Aminu Sani Jaji mai wakiltar Birnin-Magaji/Kaura a majalisar wakilan tarayya ya koka game da yawan satar ‘yan makaranta da ake yi.

A makon nan The Cable ta rahoto Honarabul Aminu Sani Jaji ya na bayanin yadda rashin hadin-kai tsakanin gwamnatoci ya jawo lalacewar tsaro.

‘Dan majalisar ya na ganin babu jituwa sosai tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi ganin yadda ‘yan bindiga su ke ta barna a jihohin Arewa.

Kara karanta wannan

Mu 100 Mu Ka Auka Makaranta, Aka Yi Awon Gaba da Yara a 2021 – ‘Dan Bindiga

‘Dan Majalisar APC
Zaman 'Yan Majalisar Tarayya Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Aminu Jaji ya koka kan ta'adin 'yan bindiga

A ‘yan kwanakin nan, an dauke daliban makaranta a Katsina, Zamfara, Nasarawa da Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan har gwamnati za ta tashi tsaye, ta tunkari lamarin tsaro da gaske, Aminu Sani Jaji ya ce a cikin watanni shida kacal, za a iya samun sauki.

Jagoran na APC a Zamfara, ya shaidawa manema labarai cewa bai goyon bayan ayi sulhu da ‘yan bindiga domin hakan bai haifar da ‘da mai ido ba.

A makonni uku da su ka gabata, an yi ta zargin juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da gwamnatin tarayya a kan lamarin sulhu

Wannan abin bai yi mani dadi ba, ganin halin tsaron da ake ciki, bai dace mu yi wasa ba.

Gwamnatin baya ta yi sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara. An yi haka a Sokoto da Katsina. Me aka samu? A karshe ba a cin ma komai ba.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Ta Ɗage Zamanta Yayin da Ɗan Majalisar APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

"Akwai karfin yakar rashin tsaro" - Jaji

Vanguard ta rahoto Hon. Jaji ya na cewa idan har ana fuskantar barazana wajen kai yara makaranta, to sha’anin ilmi zai tabarbare a Arewa.

A ra’ayin shi, ba za a ce gwamnati ba ta da karfin yakar ‘yan bindiga ba, yake cewa sai dai kurum a ce ba a ga damar kawo zaman lafiya ba.

'Yan sanda sun cafke 'masu satar mutane'

A jiya rahoto ya zo cewa rundunar DFI-IRT da DFI-STS sun yi namijin kokari wajen cafko wasu wadanda ake zargi da laifi a kasar nan.

‘Yan sanda sun cafko wanda da bakinsa ya fadi yadda su ka yi garkuwa da daliban FGC Yauri da wanda ake zargin ya sace wani bature.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng