Kwanaki Kadan da Rage Farashin Simintin, Kamfanin BUA Ya Kara Kudin Sauran Kaya

Kwanaki Kadan da Rage Farashin Simintin, Kamfanin BUA Ya Kara Kudin Sauran Kaya

  • Bayan an gama murnar sauke kudin buhun siminti, kamfanin BUA ya kara farashin wasu kayayyakinsa a Najeriya
  • ‘Yan kasuwa sun ga bambanci a farashin buhun sukari da na fulawa, sannan kudin da aka saba sayen taliya ya canza
  • Akwai yiwuwar taliyar IRS ta koma N10, 000 a hannun kananan ‘yan kasuwa a sakamakon canjin farashin da aka samu

Abuja - ‘Yan kwanaki da bada sanarwar rage kudin sarin siminti a kamfaninsa, sai aka ji BUA Group sun yi karin kudin kayan abinci.

Daily Nigerian ta gano cewa farashin da kamfanin BUA ya ke saida sukari, fulawa, taliya da sauran kaya sun tashi a halin da ake ciki.

Binciken da aka yi ya nuna farashin wadannan kaya sun tashi a kasuwa, duk da kamfanin bai fito fili ya bada sanarwar canza farashi ba.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

Kamfanin BUA
Shugaban Kamfanin BUA, Abdussamad Rabiu Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kayan BUA sun canza kudi a kasuwa

Da aka shiga kasuwar singer da ke garin Kano, an tabbatar da cewa farashin buhun sukari da na fulawa sun karu da N3, 500 da N2, 000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika an samu karin akalla N1, 000 a kan abin da ake sayen kwalin taliyar IRS.

Kafin yanzu ana saida buhun sukari ne a kan N44, 000, sai kwalin taliya a kan N8,100 yayin da ake sayen buhun fulawa a kan N32, 500.

Yanzu farashin kayan sun koma N47, 500, N9, 000 da N34, 500 wajen manyan ‘yan kasuwa.

Ana siminti ya sauka, abinci ya tashi

Wani babban dillali ya fadawa jaridar cewa kayan abincin sun tashi ne jim kadan bayan an yi sanarwar rage kudin duk buhun siminti.

‘Dan kasuwan da bai bari an kama sunansa ba, ya ce taliyar IRS Spaghetti za ta iya kai N10, 000 nan gaba kadan a wajen ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan

"Mu Na Daf Da Durkushewa", NNPC Ya Tura Sako Ga Tinubu Kan Cire Tallafi Mai A Kasar

Masu harka da kamfanin sun ce kwatsam su ka ji labarin karin, akasin yadda aka saba a baya da ake sanar da su ta kiran wayar salula.

Labarin saukake kudin simintin BUA

Legit ta fahimci ragin da BUA ya yi a kudin siminti bai sa farashi ya canza ba saboda kudin yin dakon kaya daga kamfanin zuwa garuruwa.

Idan dillali ya saye buhu a kan N3500 daga kamfanin attajirin watau Abdussamad Rabiu, zai biya kudin mota baya ga ribar da zai nema.

Cire tallafin man fetur

An rahoto Solomon Dalung ya na cewa har yanzu ‘Yan Najeriya ba su farfado daga cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi daga hawansa ba.

Dalung ya ce karya darajar Naira tamkar tura soja yaki ne babu bindiga, ya ce idan dai Tinubu bai canza salo ba, karshensa ba zai yi kyau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng