Tinubu Ya Yi Alkawarin Samar Da Ayyuka Dubu 500 A Najeriya Bayan Kammala Kamfanin Ajaokuta
- Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da himmatuwarshi na samar wa ‘yan Najeriya aikin yi a kasar musamman matasa
- Tinubu ya yi alkawarin samar da ayyuka fiye da dubu 500 da zarar kamfanin karafuna na Ajaokuta ya kammala
- Mataimakin Tinubu, Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaban ya ce Tinubu ya dage wurin inganta kasar
Jihar Kogi – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkwarin samar da ayyukan yi dubu 500 a kamfanin karafuna na Ajaokuta.
Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 8 ga watan Satumba inda ya ce ana daf da kammala aikin kamfanin a don inganta rayuwar al'umma.
Meye Tinubu ya ce kan ayyukan yi a Ajaokuta?
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsu za ta yi duk mai yiyuwa don inganta rayuwar ‘yan kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kwamitin kamfe na zaben jihar Kogi a Lokoja babban birnin jihar, cewar Vanguard.
Ya ce za su yi amfani da gudumawar da kamfanin zai bayar don inganta zuba hannun jari daga kasashen waje da samar da guraben yin kasuwanci cikin sauki.
Ya kara da cewa Tinubu ya himmatu wurin tabbatar da kammala Kogin Neja da hanyoyin Kabba zuwa Lokoja da kuma Abuja zuwa Lokoja, The Guardian ta tattaro.
Meye Kashim ya ce kan samar da ayyukan na Tinubu?
Ya ce:
“Tinubu mutum ne mai kaifin basira wanda ya ke da tsare-tsare ma su kyau inda ya himmatu wurin saka kasar nan a gurbin da ya dace da ita.
“Tinubu musamman ya na ba da karfi wurin inganta tattalin arziki a kasar wanda shi ne kinshikin ko wace kasa.”
A martaninshi, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya godewa Tinubu da ya amince da halartar bude kamfen na takarar gwamna a jihar inda ya ce gwamnatinsa ta tabuka abin a zo a gani.
Ganduje ya kaddamar da kwamitin kamfe a jihar Imo
A wani labarin, shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamitin yakin neman zaben jihar Imo.
Ganduje ya kafa kwamitin ne yayin da ake saran gudanar da zaben gwamna a watan Nuwamba a jihohin Kogi da Imo da kuma Bayelsa.
Asali: Legit.ng