Makaho Mai Maganin Gargajiya Ya Damfari Dattijuwa Naira Miliyan 19 a Jihar Ogun
- Wata dattijuwa ‘yar shekara 86 mai suna Madam Alimot ta hadu da dan damfara da ya damfare ta miliyan 19
- Wanda ake zargin makaho ne da ke bayar da maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi a jihar Ogun
- Mai maganin bayan damfararta ya kuma kwanta da diyar ta har da jikarta a lokuta da dama don yi mata magani
Jihar Ogun – Wani makaho mai maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi wanda aka fi sani da Ojunu ya damfari wata tsohuwa Naira miliyan 19.
Tsohuwar da aka damfara mai suna Madam Alimot ta kawo ‘yar ta ne don ya warkar da ita, Legit ta tattaro.
Meye ake zargin makahon da aikatawa?
A cewarta, ta rasa dukkan ‘ya’yanta 15 inda su ke rasuwa amma yanzu saura guda uku kacal shi ne ta zo neman taimako wurinshi, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar cewa matar ta samu labarin mai maganin ne a wani shiri na gidan rediyo a jihar Ogun.
A cikin shirin an bayyana mai maganin da cewa ya na warkar da dukkan wasu cututtuka da su ka gagari jama’a a cikin sauki.
Alimot ganin irin halin da ta ke ciki ta dauki lambar wayar mai maganin da wurin da ya ke zama don neman taimako.
Matar ta bar gidanta da ke yankin Mowe don zuwa wurin mai maganin da ke yankin Ogijo duk a cikin jihar.
Yadda makahon ya damfari matar makudan kudade
Makahon mai maganin ya umarci matar ta kawo saniya don a sadaukar da ita saboda iftila’in da ya sauka a gidanta.
Matar ta yi kokarin samar da kudaden da ake bukata, daga nan ne ya rin ka neman karin kudade don yin aiki, kafin wani lokaci ya karbi ya kai miliyan 19 wanda sai da ta siyar da gidajenta biyu.
Wanda ake zargin har ila yau ya kwanta da diyar matar da kuma jikarta a lokuta da dama.
Jami'an 'yan sanda sun yi artabu da 'yan fashi a Ogun
A wani labarin, wasu 'yan fashi sun kai ruwa rana da jami'an 'yan sanda a jihar Ogun.
Lamarin ya faru ne a garin Sagamu da ke karamar hukumar Sagamu a jihar yayin fashi a cikin Otal.
Asali: Legit.ng