Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Rusa Shirin N-Power Saboda Matsaloli

Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Rusa Shirin N-Power Saboda Matsaloli

  • Ministar jin kai da walwala, Betta Edu ta bayyana cewa gwamnatin Tarayya ta rusa shirin N-Power
  • Edu ta bayyana haka ne a yau Asabar 7 ga watan Oktoba yayin hira da gidan talabijin na TVC
  • Ta ce an rusa shirin har sai baba ya gani inda ta ce akwai tarun matsaloli da ke cike a shirin

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta rusa shirin N-Power har sai baba ya gani inda ta bayyana dalilan daukar wannan mataki.

Ministar jin kai da walwala, Bette Edu ita ta bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na TVC.

Tinubu ya rusa shirin N-Power saboda wasu dalilai
Gwamnatin Tarayya Ta Da Rusa Shirin N-Power. Hoto: Bette Edu, Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Edu ta ce kan rusa shirin N-Power?

Beta ta ce dalilin rusa shirin bai rasa nasaba da matsalolin da ke cike a shirin wanda aka samu a gwamnatin da ta shude.

Kara karanta wannan

Akwai Hatsari: Budurwa Ta Haura Kofar Gida Mai Hatsari Don Kai Gulma Wurin Kawarta, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar ta ce sun fara binciken yadda wasu kudade su ka bace a shirin tun bayan fara aiwatar da shirin, The Nation ta tattaro.

Ta ce masu cin gajiyar shirin da dama na tsammanin alawus a karshen wata alhali ba sa zuwa wuraren aiki, Legit ta tattaro.

Meye matsalar da saka rusa N-Power?

Ta bayyana cewa da yawa daga cikin masu cin gajiyar ya kamata sun fice tun 2022 amma su na karbar kudade.

Ta ce:

"Dole mu duba shirin N-Power saboda akwai matsaloli da dama wanda dole a dakatar da shirin kafun kammala binciken da mu ke na kudade.
"Mu na so mu san mutane nawa ne su ke cikin shirin, kuma mutane nawa ke bin bashi da yawan kudaden da su ke bi.
"Akwai abubuwa da yawa a cikin shirin saboda wasu da ya kamata sun gama cin moriya amma su na nan har yanzu a cikin tsarin."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

Shirin N-Power dai an kirkiro ta ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari don rage talauci musamman a tsakanin matasa.

Masu cin gajiyar shirin N-Power sun bukaci a biya su alawus

A wani labarin, matasa masu cin gajiyar N-Power sun roki Shugaba Tinubu da ya tausaya a biya su alawus da su ke bin bashi.

Matasan sun bayyana cewa wasu a cikinsu na bin bashi tun watan Janairu kuma har yanzu shiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.