Uwar Gulma Ta Haura Kofar Gida Don Kai Gulma Ga Kawarta A Gidan Haya

Uwar Gulma Ta Haura Kofar Gida Don Kai Gulma Ga Kawarta A Gidan Haya

  • Faifan bidiyon Wata budurwa ya yadu bayan ganin ta na haura kofar gida don kai gulma
  • Kawarta da ke cikin gidan ta rike mata matakala don saukowa lafiya da kuma ba da labarin
  • Matar da ke gidan ta bayyana dalilin da ya sa aka kulle gidan yayin da mutane su ka tofa albarkacin bakinsu

Wata budurwa ta ba da mamaki yayin da ta tsallaka katanga don kai gulma ka kawarta.

An yada faifan bidiyon inda budurwar ke tsallake kofar shiga gidan duk da wayoyin da ke kai kawai don gulma.

Yadda budurwa ta haura kofar shiga gida don isar da sakon gulma ga kawarta
Uwar Gulma Ta Haura Kofar Gida Don Kai Rahoto. @stainlessgoody.
Asali: TikTok

Meye budurwar ta yi a faifan bidiyon?

A bidiyon da aka yada na TikTok, kawar tata na rike da matakala don taimaka mata saukowa lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu

@stainleaagoody ne ya yada bidiyon wanda ya jawo kace-nace tsakanin mutane wanda da yawa ke ba ta shawara na ta yi hankali da wandonta.

Matar da ke cikin gidan ta bayyana cewa an rufe kofar gidan ne shi ya sa kawar tata ta hauro don ba ta labari.

Ta ce:

"An rufe kofar 'gate' din ne da kaca da kuma kwado, kun san ba karamin abu ba ne zai saka 'yan sanda rufe kofa har da kwado."

Ku kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane kan faifan bidiyon

Mutane da dama sun yi martani bayan ganin yadda matar ke haura kofar inda su ke ba ta shawara ta yi hankali da jikinta.

Ada:

"Damuwa na wayoyin wuta da ke jikin kofar ne."

Everything_Dora:

"Lallai gulmar za ta yi zaki, amma ki kula da wandonki."

Simdi:

"Ko ma meye ne ya kamata ta jira."

Author-Miran22:

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Musulunci Yayin Da Su Ke Raka Gawa Makabarta, Bayanai Sun Fito

"Dan Allah ka da ki sake irin wannan kasadar."

iamfemlltele:

"Ta yi hankali da arzikinta dai kam."

Matashi ya hargitsa Intanet bayan wallafa bidiyo da mahaifiyarsa

A wani labarin, wani matashi ya girgiza Intanet bayan ya wallafa faifan bidiyo tare da mahaifiyarsa.

Matashin na mamaki ganin yadda 'yar karamar mata irin wannar ace ta haife shi duk girman nan nasa.

Matashin ya kalli mahaifiyar cikin mamaki da waswasin anya kuwa ita ta haife shi yadda ya ke gabjejen matashi amma ace 'yar matar nan ne ta haife shi abun da mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel