Kungiyar MURIC Ta Yabawa Abba Kabir Yusuf Kan Haramta Amfani Da Wasu Littattafai A Makarantu
- Kungiyar MURIC a jihar Kano ta yabawa Gwamna Abba Kabir wurin haramta amfani da wasu littattafai a makarantu
- Kungiyar ta ce wannan mataki na gwamnatin jihar ya zo a dai-dai ganin yadda tarbiyya me kara tabarbarewa a harkar Ilimi
- A jiya Alhamis ne gwamnatin jihar ta haramta amfani da wasu littattafai da ke dauke da misalan da ba su dace ba a koyar da yara
Jihar Kano - Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta yaba wa Gwamna Abba Kabir na haramta amfani da wasu littattafai a makarantun Nursery da firamare a jihar.
Shugaban kungiyar a jihar, Hassan Indabawa shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 6 ga watan Oktoba.
Meye MURIC ta ce kan wannan mataki na Abba Gida Gida?
Ya ce wannan mataki ya yi dai-dai wurin dakile rashin tarbiyya da ke cikin litattafan.
Kano: Abba Gida Gida Ya Amince Da Biyan Makudan Kudade Ga Daliban Da Ke Jami'o'in Najeriya, Ya Bayyana Dalili
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa wannan mataki na Abba Gida Gida ya yi saboda a lokacin da ya dace ne ganin yadda tarbiyya ke kara lalacewa musamman a harkar ilimi.
Sanarwar ta ce:
"A dalilin haka, ya kamata iyaye da malamai da kuma dalibai su goyi bayan wannan mataki don dakile lalata tarbiyya a tsakanin matasa."
Indabawa ya ce Kungiyar MURIC na gaba-gaba wurin tabbatar da an dakile rashin da'a a tsarin ilimi a kasar.
Wane mataki Abba Gida Gida ya dauka a Kano?
Ya ce:
"MURIC ta yabawa gwamnan jihar Kano wurin haramta amfani da wasu alamomin koyarwa da ke dauke da abubawa masu ruguza tarbiyya a makarantu.
"Yan Najeriya sun sani a shekaru 20 da su ka wuce akwai littattafai kamar su Things Fall Apart da Macbeth da littafin adabi na Turanci da sauransu da aka cire su daga tsarin ilimi."
Ya ce akwai kuma wasu littattafai da su ke dauke da misalan iskanci wadanda ke lalata tarbiyyar matasa a makarantu, Daily Nigerian ta tattaro.
Idan ba a manta ba a jiya ne gwamnatin jihar Kano ta haramta amfani da wasu littattafai a makarantun Nursery sa firamare da kuma sakandare da ke dauke da misalan da ba su dace ba.
Abba Gida Gida ya dakatar da shugabannin makarantu 2 a Kano
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir ya dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare biyu a Kano kan rashin bin doka.
Daraktan wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilimi, Balarabe Kiru shi ya bayyana haka inda ya ce wadanda ake zargin sun karya doka.
Asali: Legit.ng