An bayyana ranar buɗe makarantun gaba da sakandare a jihar Kano
- Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa za a bude makarantun gaba da sakandare a jihar a ranar 26 ga watan Oktoba
- Kwamishinan Ilimin manyan makarantu na jihar, Dakta Mariya Bunkure ce ta bada sanarwar
- Dakta Bunkure ta ce gwamnatin jihar ta yi feshin magani a makarantun sannan ta tanadi matakan daƙile yaɗuwar korona
Gwamnatin jihar Kano ta tsayar da ranar 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za ta buɗe makarantun gaba da sakandare bayan watanni bakwai suna rufe.
Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu a jihar, Dakta Mariya Bunkure ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a daren ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Hotuna: Ango ya garzaya wurin zanga-zangar EndSars daga wurin ɗaurin aurensa
A ranar Litinin ne jihar ta buɗe makarantun Nursery, Frimare da Sakandare amma banda Kasa da SS1.
Bunkure ta ce gwamnatin ta tanadi matakai na kare yaɗuwar korona ta suka hada da feshin magani da samar da kayan kariya.
"Mun yanke shawarar bude makarantu duba da sauƙin masu kamuwa da Covid 19 da muka samu tare da umurnin kwamitin shugaban kasa ta yaƙi da korona da ta ce ana iya bude makarantu.
KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi
Makarantun gaba da sakandare na jihar sun hada da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, Ƙwalejin Ilimi ta Sa'adatu Rimi, Makarantar Koyon aikin masu jinya, Jami'ar Maitama Yusuf, Kwalejin Fasaha ta Kano da sauransu.
A wani rahoton, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.'
Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng