Sanata Zam Ya Bayyana Cewa Iyayensa Na Cikin Kuncin Rayuwa A Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Benue

Sanata Zam Ya Bayyana Cewa Iyayensa Na Cikin Kuncin Rayuwa A Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Benue

  • Sanata Titus Zam ya koka kan yadda mutane ke halin kunci a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Benue
  • Zam ya ce ya yi zabe a matsayin mamban sansanin 'yan gudun hijira saboda iyayensa na daga cikin wadanda ke sansanin
  • Sanatan ya bukaci majalisar ta umarci ma'aikatar jinkai don kawo dauki na magani da kayan tallafi

FCT, Abuja - Wani Sanata a jihar Benue, Titus Zam ya bayyana cewa iyayensa na cikin kunci a sansanin 'yan gudun hijira a jihar.

Sanatan wanda ke wakiltar Arewa maso Yammacin jihar ya ce hakan ya faru sanadiyyar hare-haren 'yan bindiga a shekarar 2022, Legit ta tattaro.

Sanata a Najeriya ya ce iyayensa na shan bakar wahala a sansanin 'yan gudun hijira
Sanata Zam nuna damuwa kan iyayensa da ke sansanin 'yan gudun hijira. Hoto: Akawe Terngu Moses.
Asali: Facebook

Meye Sanatan ya ce kan sansanin gudun hijira?

Zam ya ce ya yi zabe a matsayin mamba a sansanin a zaben aka gudanar a wannan shekara.

Kara karanta wannan

An Saida Fetur a Kan N415 a Maimakon N615 da Attajiri Ya Tausayawa Mutanen Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A yanzu da na ke magana da ku, iyayena su na can cikin kuncin rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira.
"A matsayina na Sanata na yi zabe a matsayin mamba a sansanin 'yan gudun hijira a zaben da aka gudanar a wannan shekara."

Ya kara da cewa mutane fiye da miliyan daya da dubu 500 ke sansanin 'yan gudun hijira saboda hare-haren 'yan bindiga a 2022, cewar Premium Times.

Ya ce yara 560 da ke sansanin na fama da yunwa tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba na shekarar 2022.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin gabatar da kuduri a majalisar Dattawa a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba.

Wane roko Sanatan ya yi ga majalisa kan 'yan gudun hijira?

Sanatan ya ce 'yan bindigan sun shafe shekaru bakwai su na kai wa manoma hari a kananan hukumomin Gwer ta Yamma da Makurdi da Guma.

Kara karanta wannan

Murna Yayin Da Kwamishina A Arewa Ya Shaki Iskar 'Yanci Bayan Sace Shi Da Aka Yi, Iyalansa Sun Yi Bayani

Ya bukaci majalisar ta umarci ma'aikatar jin kai don taimaka musu da kayan tallafi da magani.

Ya kuma roki hafsan tsaron soji da ya tabbatar da tsaro don dawowar 'yan sansanin gudun hijira zuwa gidajensu.

'Yan bindiga sun sace kwamishina a jihar Benue

A wani labarin, masu garkuwa sun sace kwamishinan yada labarai a jihar Benue, Matthew Abo a gidansa da ke Zaki-Biam.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da sace kwamishinan a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.