Gwamnan Jihar Osun Ya Sake Sanya Dokar Kulle a Wasu Kananan Hukumomi 2 Na Jihar

Gwamnan Jihar Osun Ya Sake Sanya Dokar Kulle a Wasu Kananan Hukumomi 2 Na Jihar

  • Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya sake sanya dokar hana fita a wasu ƙananan hukumomi guda biyu na jihar
  • Aɗeleke ya sanya dokar hana fitan ne biyo bayan rikicin filaye da ya sake ɓarkewa a tsakanin al'ummomin ƙauyukan Ilobu da Ifon
  • Sanarwar sanya dokar hana fitan wacce ta fito ta hannun kwamishinan watsa labarai na jihar, ta ce dokar ta koma daga ƙarfe 6:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na safe

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta sanya sabuwar dokar hana fita a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu na jihar, biyo bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummar ƙauyukan Ilobu da Ifon.

Idan dai za a iya tunawa gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu a farkon watan Satumba, bayan da aka samu rikici tsakanin ƙauyukan biyu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Farmaki a Jami'ar Usmanu DanFodiyo? VC Ya Yi Karin Haske

Gwamna Adeleke ya sake sanya dokar hana fita
Gwamna Adeleke ya sake sanya sabuwar dokar hana fita a wasu kananan hukumomi biyu Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Daga baya an sassauta dokar hana fita bayan hankula sun kwanta a yankin, rahoton Tribune ya tabbatar.

Meyasa aka sake sanya dokar?

Sai dai, wata sanarwa da Kolapo Alimi, kwamishinan watsa labarai da wayar da kan jama’a na jihar, ya fitar a ranar Laraba, ta ce Adeleke ya bayar da umarnin a mayar da dokar hana fita a ƙananan hukumomin biyu, biyo bayan rikicin da ya ƙara ɓarkewa a ƙauyukan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Biyo bayan sake ɓarƙewar rikicin ƙabilanci tsakanin mutanen ƙauyukan Ilobu da Ifon, gwamnatin jihar Osun ta ba da umarnin dokar hana fita ta cigaba da aiki a ƙauyukan da lamarin ya shafa."
"Lokacin dokar hana fitan ya koma ƙarfe 6:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe. Za a taƙaita zirga-zirgar mutane da ababen hawa yayin dokar har sai an samu sabuwar sanarwa."

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

"Hakan wajibi ne domin daƙile yunƙurin lalata rayuka da dukiyoyi a cikin wannan lokacin, saboda rikicin filaye."
"Duk wanda aka kama yana yawo a ƙananan hukumomin Irepodun da Orolu a lokacin dokar hana fitan, za a cafke shi tare da fuskantar hukunci."

Gwaman Ottu Ya Sanya Dokar Kulle

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Ottu, ya sanya dokar hana fita a wasu ƙauyuka na jihar.

Gwamnan ya sanya dokar kullen ne a ƙauyukan Ugaga, Igbekurekor, Benekaba da Ijama na ƙaramar hukumar Yala ta jihar, biyo bayan ɓarkewar rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel