Minista Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Mai Da Hankali Kan Gina Kasa Madadin Matsalar Takardun Tinubu

Minista Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Mai Da Hankali Kan Gina Kasa Madadin Matsalar Takardun Tinubu

  • Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali wurin ci gaban kasa
  • Tuggar ya ce bai kamata matsalar takardun karatun Tinubu ya kawar musu da hankali wurin kawo ci gaban kasa ba
  • Ministan ya bayyana cewa ba su da lokacin bata wa ganin yadda Tinubu ya shafe shekaru ya na siyasa ba tare da wannan matsalar ba

FCT, Abuja - Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ya roki 'yan Najeriya su kau da kai ga maganar takardun karatun Tinubu.

Ya ce ya kamata 'yan kasar su mai da hankali ne wajen gina kasa kawai, Legit ta tattaro

Minista Tuggar ya bukaci 'yan Najeriya su mai da hankali wurin gina kasa
Minista Tuggar ya yi martani kan takardun karatun Tinubu. Hoto: Facebook.
Asali: UGC

Meye Tuggar ya ce kan takardun Tinubu?

Tuggar ya bayyana haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a yau Laraba 4 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Muhammadu Buhari: Babban Sakona Ga Mutanen Najeriya a Ranar Murnar 'Yancin Kai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matsalar takardun Tinubu ba abin tashin hankali ba ne ganin yadda ya dade a siyasa har ya yi gwamna wa'adi biyu.

Ya ce abin da ya kamata 'yan kasar su mai da hankali shi ne gina kasa musamman halin tattalin arziki da ake ciki da kuma yawan jama'a.

Yusuf ya ce wasu ne ke amfani da maganar takardun don kawar da hankula kan ci gaban kasa.

Ya yi bayanin yadda Tinubu ya shafe shekaru a siyasa

Ya ce:

"Babu wanda ya ke bata lokaci a maganar shaidar karatun Tinubu, mutumin da ya shafe shekaru ya na siyasa, ya yi gwamna har wa'adi biyu.
"Haka aka ta yi wa Buhari kan cewa bai kammala makarantar sakandare ba, mutumin da ya ke da abokai a makaranta kuma shugaban dalibai.
"Wannan wani salo ne na kau da tunanin mutane daga mai da hankali kan ci gaban kasa, ba mu da lokacin bata wa a yanzu."

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Ya ce a yanzu bai kamata 'yan kasar su ba ta lokaci kan wannan matsalar ba, Daily Trust ta tattaro.

Ya kara da cewa akwai matsaloli da su ke damun kasar kamar su tabarbarewar tattalin arziki da yawan jama'a.

Tinubu ya maye gurbib El-Rufai a mukamin minista

A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon minista a madadin Nasir El-Rufai a mukamin minista.

Tinubu ya nada Balarabe Abbas a matsayin minista daga jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.