EFCC Ta Samu Nasara Kan Alison-Madueke, Ana Kokarin Taso Keyar Tsohuwar Minista
- Ana shari’a tsakanin Diezani Alison-Madueke da gwamnatin Birtaniya a wani kotu da ke Westminster
- Tuhumar da ake yi wa ‘yar siyasar Najeriyar ta shafi bada cin hancin makudan kudi a birnin Landan
- Zargin sun sha bam-bam da wadanda ake yi mata a gida, EFCC ta ce za a maido Alison-Madueke gida
United Kingdom - Tsohuwar ministar harkokin man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban kotun majistaren Westminster a Ingila.
Ana zargin Madam Diezani Alison-Madueke da bada cin hancin £100,000, Punch ta ce a kan haka aka gurfanar da ita a gaban kotu a ranar Litinin.
Alkalin Westminster, Michael Snow ya bada belin ‘yar Najeriyar a kan fam £70,000, idan aka yi lissafi a Naira, kudin belin ya haura N67,392,598.
Diezani Alison-Madueke ta samu beli
Kafin ta bar kuliya, an yanke hukunci cewa sai Alison-Madueke ta bada jinginar wadannan kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka, Mai shari’a Snow ya kakabawa Alison-Madueke takunkumi ta yadda babu inda za ta iya zuwa tsakanin karfe 11:00 zuwa 6:00 na safe.
Tsohuwar ministar sufuri da harkokin man fetur ta Najeriyar za rika yawo da wata sarka mai aiki da lantarki da za ta rika nuna inda ta ke ko yaushe
Wanda ake tuhuma ba ta yi magana tukuna ba a kotu, amma Reuters ta ce Madam Alison-Madueke ba za ta amsa laifin da ake zarginta da aikatawa ba.
A ranar 30 ga watan Oktoba, za a cigaba da sauraron wannan kara a kotun na Southwark Crown.
EFCC ta yi farin ciki da tsare Alison-Madueke
The Cable ta rahoto EFCC mai yaki da rashin gaskiya a Najeriya ta na mai maraba da hukuncin da Alkalin kotun ya fara yankewa a shari’ar da ake yi.
Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya ce su na sa ido a kan abin da ke wakana a kotu, a gida kuwa ana zargin ta saci fiye da fam $72m.
Mista Dele Oyewale ya kara da cewa sun samu damar dauko tsohuwar ministar daga Ingila, kuma an fara hobbasa domin yin shari’a da ita a kasarta.
Bola Tinubu ya ba Fasua mukami
Rahoto ya zo cewa Shugaba Bola Tinubu ya zakulo Tope Fasua, ya aika shi ofishin Kashim Shettima ya zama mai bada shawara kan tattalin arziki.
Tope Fasua shi ne shugaban kamfanin Global Analytics Consulting Limited, ya kware a harkar tattali, ya taba yin takara da Muhammau Buhari.
Asali: Legit.ng