Dantata Ya Kirkiri Sabon Bankin Yanar Gizo Da Zai Fafata Da Opay, Moniepoint, Kuda

Dantata Ya Kirkiri Sabon Bankin Yanar Gizo Da Zai Fafata Da Opay, Moniepoint, Kuda

  • Najeriya ta sake samun sabon bankin zamani na yanar gizo wanda zai taimaka wurin kawo sauki a harkar cinikayya na kudade
  • Sabon bankin mai suna Kayi wanda Alhaji Saadina Dantata ya kirkira ya samu sahalewar wasu kasashe na hannun jari kamar Saudiyya
  • Sabon bankin na dan kasuwar da ke Kano zai fafata da sauran bankunan yanar gizo kamar su Kuda da Opay da Moniepoint da sauransu

FCT, Abuja - Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Bosun Tijjani ya kaddamar da wani bankin zamani na yanar gizo mai suna 'Kayi Bank'.

Bankin wanda attajirin dan kasuwa, Alhaji Saadina Dantata ya dauki nauyi an kaddamar da shi a Abuja a makon da ya gabata.

Dantata ya bude sabon banki mai suna Kayi da zai yi gogayya da Opay, Moniepoint, Kuda
Alhaji Dantata Ya Kirkiri Sabon Bankin Yanar Gizo. Hoto: Kayi Bank.
Asali: Twitter

Meye kudirin bankin Kayi na Dantata?

Legit ta tattaro cewa bankin Kayi kasashe da dama kamar su Daular Larabawa da Turkiyya da Saudiyya sun zuba hannun jarinsu a ciki.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya ke magana, Dantata ya ce an samar da kamfanin ne don shawo kan matsalar fasaha da tsaro da kuma inganta jin dadin kwastomomi.

Ya ce:

"Mu na inganta rayuwar murane a fadin Nahiyar Afirka wurin samar da cinikayya ta kudade cikin sauki.
"Burinmu shi ne samar da asusun bankuna ga wadanda ba su da shi da wadanda ke kasashen ketare."

Wane amfani bankin Kayi zai yi ga al'umma?

Minista sadarwa ya yabawa mamallakin bankin Kayi inda ya ce hakan zai karawa gwamnatin Bola Tinubu karfi wurin tabbatar da samar da ayyukan yi.

The Nation ta tattaro cewa ministan ya godewa kamfanin wurin samar da sauki ga masu tasi da adaidaita sahu.

A tsarin kamfanin, zai samarwa masu tasi din saukin yadda za su sayi mai a wasu gidaje tare da biyan kudin bayan kwana daya don rage radadin cire tallafi.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

CBN ya karyata jita-jitar dakatar da Opay, PalmPay

A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya karyata cewa ya dakatar da ayyukan bankunan zamani na yanar gizo a kasar.

Bankunan da ake magana sun hada da Opay da PalmPay bayan gano cewa su na da hannu a aikata damfara.

Bankin ne ya fitar da sanarwar inda ya bukaci alumma su yi watsi da wannan karairayi da ake yadawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.