Damar Cire Kuɗi: Bankuna Sun Bi Umarnin CBN Na Fitowa Aiki a Karshen Mako

Damar Cire Kuɗi: Bankuna Sun Bi Umarnin CBN Na Fitowa Aiki a Karshen Mako

  • Bankunan kasuwanci a faɗin Najeriya sun bi umarnin CBN zasu fito aiki a ranakun Asabar da Lahadi
  • CBN ya tabbatar da cewa ya fito da takardun naira da ke ajiye a wurinsa kuma ya tura su ga bankuna
  • Da yawan Bankuna sun tura wa kwastomominsu sakonnin Email na lokacin da zasu same su a ranakun Asabar da Lahadi

Lagos - A yunkurin bin umarnin babban bankin Najeriya (CBN), bankunan kasuwanci sun sanar da cewa rassansu zasu fito aiki domin mutane su aje ko cire kuɗi a ranakun karshen mako.

The Cable ta rahoto cewa tun da safiyar ranar Jumu'a, CBN ya sanar da cewa ya kwashe kuɗaɗen da ake hannunsa ya tura wa bankuna a faɗin kasar nan.

Bankunan Najeriya.
Damar Cire Kuɗi: Bankuna Sun Bi Umarnin CBN Na Fitowa Aiki a Karshen Mako Hoto: thecable
Asali: Facebook

Domin sauƙaƙa wa al'umma su samu takardun kuɗi a hannunsu, CBN ya umarci bankuna da su saurari kwastomominsu a ranakun Asabar da Lahadi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Da alamu an kusa daina ganin tsabar kudi, CBN zai iya kakaba wata hanyar biya

Awanni bayan wannan umarni, bankuna suka fara aika sakonnin Email, suna faɗa wa kwastomominsu su je rassan bankuna a lokacin da aka ware ranar Asabar da Lahadi domin cire kuɗi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sakonnin da bankunan GT da Union suka aika wa mutane a Legas, sun ce mutane na ɗa ikon zuwa kowane reshen banki a faɗin kasa don cire kuɗi daga 9:00 na safe zuwa 4:00 na yanma.

"Dukkan rassan bankunanmu zasu buɗe ranar Asabar da Lahadi, 25 da 26 ga watan Maris, 2023 daga karfe 9:00 na safe zuwa 4:00 na yamma domin ajiya da cire kuɗi," inji Union Bank.

A wani ɓangaren kuma Standard Chartered Bank ya ce kwastomominsa zasu samu damar biyan buƙatunsu daga ƙarfe 10 na safe zuwa 3 na yamma.

"Domin sauƙaka kuncin karancin takardun naira, Muna sanar muku cewa zamu buɗe rassanmu a ranakun ƙarshen mako domin cire kuɗi daga asusu ko kawo ajiya."

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Mutane 79 da Suka Haddasa Rikici da Karya Doka Yayin Zaɓen Gwamna A Jihar Arewa

"Zamu yi aiki ranar Asabar da Lahadi 25 da 26 ga watan Maris, 2023 daga karfe 10:00 na safe zuwa karfe 3:00 na rana," inji Email din da suka tura wa mutane.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani ma'aikacin First Bank a garin Zariya, ya ce yana da yakinin an tura kwastomomi saƙo domin ranar Jumu'a sun samu umarni daga manyansu cewa za'a yi aiki a karshen mako.

"Na san mutane zasu samu sakonni daga First Bank, a ɓangaren mu tun kafin mu tashi aiki ranar Jumu'a aka faɗa mana akwai aiki ranar Asabar da Lahadi karfe 10 zuwa 1:00 na rana," inji shi.

Haka nan wani Kwastoman bankin, Abdulhafiz Tukur, ya shaida wa wakilin mu cewa an turo masa sakon cewa rassan First Banki a faɗin Najeriya zasu biya kuɗi ranar Asabar da Lahadi.

Bugu da ƙari, wakilinmu ya ci karo da saƙon bankin, wanda ya ce:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Najeriya Sun Halaka Babban Ɗan Ta'adda da Wasu Mayaƙa Sama da 40 a Arewa

"Bisa alkawarin mu na sanya ku a sahun farko, muna farin cikin sanar daku cewa rassanmu zasu buɗe ranakuna 25 da 26 ga watan Maris, 2023 daga 10:00 na safe zuwa 1:00 na rana domin biyan bukatunku," inji First Bank

Gwamnan CBN Ya Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Abu 1

A wani labarin kuma Gwamnan CBN ya baiwa yan Najeriya hakuri kan matsalar da suka fuskanta yayin tura kuɗi ta Intanet

Godwin Emefiele ya ce wasu matsaloli ne suka nemi fin karfinsu, amma zuwa yanzun suna kokarin shawo kansu baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel