An samu sabanin ra'ayi tsakanin gwamnati da iyayen 'yan Mata kan koma wa makarantar Dapchi

An samu sabanin ra'ayi tsakanin gwamnati da iyayen 'yan Mata kan koma wa makarantar Dapchi

Gwamnatin tarayya da iyayen 'yan matan Dapchi da aka sako sun raba gari a yayin da gwamnati ke kokarin sanya daliban su koma makarantar su ta Dapchi domin ci gaba da karatu da daukan darussa, iyayen 'yan matan sun ce ba za ta sabu ba.

A yayin da iyayen matan suka lashi takobbi cewa 'yan matan su ba za su koma wannan makaranta ta Dapchi ba, gwamnatin tarayya ta hau kujerar naki da cewar 'yan matan sai sun koma kuma sun ci gaba da karatun su a mako mai gabatowa a makarantar da aka yashe su a ranar 19 ga watan Fabrairu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne 'yan Boko Haram suka dawo da wannan dalibai yayin da kuman aka garzaya da su zuwa birnin tarayya domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ta makon da ya gabata.

Shugaba Buhari tare da 'yan Matan Dapchi da aka sako yayin ziyara a fadar Villa
Shugaba Buhari tare da 'yan Matan Dapchi da aka sako yayin ziyara a fadar Villa

Rahotanni sun bayyana cewa, 5 daga cikin 'yan mata 110 da aka yashe sun rigamu gidan gaskiya a yayin ta'addanci na garkuwa da su tun a ranar da lamarin ya afku, inda 'yan ta'addan su ka dawo da ragowar dalibai 104 tare da ci gaba da garkuwa da wata daliba daya mai sunan Leah Sharibu kasancewar ta 'yar addinin Kirista kuma ta ki amsar Musulunci da suka yi ma ta tayin sa.

Shugaban kungiyar iyayen matan, Mallam Bukar Kachalla, shine ya bayyana wannan matsaya ta iyayen a wata ganawar wayar salula da manema labarai.

Mallam Bukar ya bayyana cewa, ba zai yiwu su sake tura 'ya'yayen su wannan makaranta alhalin ba su da tabbacin tsaro wanda ka iya jefa yaran su cikin hadari.

KARANTA KUMA: Jerin kasashe 11 da su ka ki aminta da yarjejeniyar yankin cinikayya a nahiyyar Afirka

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa, wannan shawara da iyayen yaran suka yanke ta zo ne da sanadin shugaban jami'ar Nigerian Turkish Nile University, Farfesa Huseyin Sert, na bayar da gudunmuwa ta daukar nauyin 'yan matan domin ci gaba da karatun su.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fede wa jam'iyyar PDP biri har wutsiya akan zargin da ta ke yiwa APC da hukumar zabe ta kasa na shirya magudi a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel