Mahaifiya Ta Cafke Wanda Ya Yi Garkuwa Tare Da Halaka Yarta a Zariya

Mahaifiya Ta Cafke Wanda Ya Yi Garkuwa Tare Da Halaka Yarta a Zariya

  • Wani mai garkuwa da mutane ya shiga hannun jami'an tsaro bayan mahaifiyar yarinyar da ya sace ta gane shi
  • Mahaifiyar yarinyar ta gane shi ne lokacin da suka je kai masa kuɗin fansan da buƙata kafin ya sako yarinyar
  • Wanda ake zargin ya amsa cewa ya sace yarinyar tare da halaka ta da binne gawarta a cikin gidansa

Zariya, jihar Kaduna - Wata mata a Zariya ta yi nasarar cafke wani da ake zargin ya sace ƴarta tare da neman kuɗin fansa domin ya sake ta.

Majiyar tsaro ta ce ana zargin Aminu Ibrahim mai shekaru 35 da sace wata budurwa mai suna Fatima Adamu mai shekara 23, daga bisani kuma ya halaka ta tare da binne gawar ta, cewar rahoton Daily Trust.

Mahaifiya ta cafke wanda ya yi garkuwa da diyarta
Mahaifiya ta kama wanda ya yi garkuwa da yarta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Da take jawabi a gidanta, mahaifiyar matashiyar da aka yi garkuwa da ita, Malama Nana Fatima, ta ce ba za ta iya yin ƙarin bayani ba saboda tsananin baƙin cikin da take ciki.

Kara karanta wannan

“Matata Na Zarginmu”: Alhaji Birni Ya Yi Wa Budurwa Alkawarin Miliyan 3 Da Tafiya Waje Idan Ta Boye Alakarsu

Sai dai wata ƙanwar mamaciyar mai suna Hajara Adamu ta bayyana cewa Fatima ta yi tafiya ne zuwa Kaduna da nufin shafe kwanaki huɗu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajara ta ƙara da cewa lokacin da aka yi tsammanin dawowar ta bata dawo ba, sai aka yi ta kiran ta a waya amma ba ta ɗauka ba.

Ta bayyana cewa daga baya ne wani mutum ya ɗauki wayar ya shaida musu cewa shi ne ya sace Fatima kuma ya nemi N100,000 a matsayin kuɗin fansa.

Ta yaya aka cafke wanda ake zargin?

A cewar iyalan, an tara kuɗin sannan aka ba wanda ake zargin a wani wuri da ya tsara a unguwar Wusasa, Zariya.

Hajara ta cigaba da bayyana cewa wanda ake zargin ya yi alkawarin sakin Fatima a ranar amma bai yi hakan ba. Bayan kwana uku ya sake kira ya buƙaci a mara masa N100,000.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Ɗana Tarko, Sun Yi Garkuwa da Babban Jami'in Sojojin Najeriya

A nan ne mahaifiyar da Hajara bayan sun sayar da filinta, sai suka kai kuɗin wurin haɗuwarsu a Wusasa, inda ta gane wanda ake zargin bayan ta yi arba da shi lokacin da yake sauka daga kan babur ɗin ɗan Achaɓa.

Nan take Fatima ta fara neman taimako, lamarin da ya ja hankalin jama'a zuwa wajen da lamarin ya faru, daga bisani kuma suka taimaka wajen cafke wanda ake zargin tare da miƙa shi ofishin ƴan sanda na Dan Magaji domin yi masa tambayoyi.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya kai ƴan sanda zuwa gidansa da ke Limancin Iya, Zariya, inda ake zargin ya binne gawar Fatima.

A yayin gudanar da binciken farko, Ibrahim ya bayyana cewa yana da hannu wajen yin garkuwa da mutane a yankin.

Ya bayyana cewa marigayiyar ta rasu a hannunsu kuma sun binne ta a gidansa dake Limanchin Iya.

Kara karanta wannan

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Shiga Bakin Ciki Bayan Siyar Da Wayarta Don Saurayinta, Bidiyon Ya Yadu

Muƙaddashin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da kama wanda ake zargin kuma ya ce ana cigaba da gudanar da bincike.

Yan Bindiga Sun Sace Mutane a Neja

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa mutane da dama a wani sabon hari a jihar Neja.

Yan bindigan sun yi garkuwa da aƙalla mutum 31 a ƙauyukan Kabula da Zagzaga a ƙaramar Munya ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng