Jiga-jigan APC Sun Ba Tinubu Shawarwari 5 Don Hana Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago Na TUC da NLC
- Jiga-jigan jam’iyyar APC sun bukaci kungiyoyin kwadago da su yi hakuri da gwamnatin Bola Tinubu
- Jiga-jigan siyasar sun bukaci NLC da TUC da su yi la’akari da kokarin da shugaban kasa ke yi na dakile wahalar tasirin cire tallafin.
- A zantawarsu da Legit.ng sun kuma da da shawarwari 5 da Tinubu zai iya bi domin gyara kasar nan
Jihar Oyo, Ibadan – Wasiu Olawale Sadare, kakakin jam’iyyar APC na jihar Oyo, ya bayyana abubuwa biyar da ya kamata shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi domin kare tattalin arzikin Najeriya daga kara durkushewa.
Jigon na jam’iyyar APC ya bayyana cewa idan aka dauki matakan, za a samu mafita a gwamnatin Tinubu wajen biyan bukatun kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC tare da dakile shirin yajin aikin da suke shirin yi.
Batun shiga yajin aiki a mako mai zuwa
Idan baku manta ba, kungiyoyin biyu sun shirya shiga yajin aiki, wanda suka farawa daga ranar Talata, 3 ga Oktoba, 2023, duk da rokon da gwamnati ta yi na su dakata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin kungiyoyin sun yanke shawarar katse aiki a fadin kasar nan idan jawabin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba bai magance bukatunsu ba.
A bayyane yake, Najeriya na ci gaba da fuskantar bakar wahalar tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa Tinubu ya yi.
Haka nan, jigon APC Francis Okoye ya roki 'yan kwadago su yi hakuri, gwamnati ta yi alkawarin kara albashi.
Shawarwarin da aka ba Tinubu guda 5
Jigon na APC ya bayyana, cewa akwai bukatar gwamnati ta yi abubuwa guda biyar kamar haka:
1. Ya kamata gwamnatin Tinubu ta tsaftace fannin makamashi, ta kuma tabbatar da cewa 'yan kasa sun rage dogaro da shigo da mai.
2. Na biyu, ya kamata CBN ya magance matsalolin da suka shafi kudin kasar nan; ta yadda kudaden ketare za su tsaya kunnen doki da Naira.
3. Na uku, ya kamata a duba batun samar da abinci da nufin ganin ‘yan Najeriya ba su kwana da yunwa ba.
4. Na hudu, a sanya matsakaitan ma’aikaci su samu wadataccen albashi ba tare da bata lokaci ba, kuma a kowanne fanni na aiki.
5. A karshe dole ne a farfado da tattalin arzikin kasar nan cikin gaggawa don samar da damammakin samar da kayayyaki a cikin gida da kuma samar da matasa marasa aikin yi da ke shirye su nemi haliliyarsu.
Za mu bi umarnin NLC wajen shiga yajin aiki, mai makarantar kudi a Gombe
A bangare guda, Legit Hausa ta tattauna da wata mai makarantar kudi a jihar, Z.A Abubakar, inda tace za su bi umarnin NLC na shiga yajin aiki.
A cewarta:
"Ai yaji ya shafi kowa, ya shafi iyayen yara don haka muma ya shafe mu, idan basu samu ba, mu ma bamu samu ba.
"Allah dai yasa gwamnati ta gane sannan mu kuma mu fahimci inda aka dosa don warware matsalolin kasarmu."
Asali: Legit.ng