“Ana Ruwa Amma Duk Da Haka Akwai Wuta”: Matashi Dan Najeriya Da Ke Turai Ya Cika Da Mamaki

“Ana Ruwa Amma Duk Da Haka Akwai Wuta”: Matashi Dan Najeriya Da Ke Turai Ya Cika Da Mamaki

  • Wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya ya yi korafi kan ruwan sama mara yankewa da aka zuba a kasar Turan
  • Matashin ya ce ya lura an shafe tsawon kwanaki bakwai ana zabga ruwan sama, lamarin da ya haifar da sanyi
  • Ya ce babban abun da ya ba shi mamaki shine cewa ba dauke wuta ba duk da ruwan sama mara yankewa da ake ta yi

Wani dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya ya cika da mamakin dalilin da yasa ba a dauke wutar lantarki ba a yankin da yake duk da ruwan sama mara yankewa da ake ta yi.

Mutumin ya cve an jera tsawon kwana bakwai ana zuba ruwa a yankin da yake, amma ya lura cewa har lokacin akwai wutar lantarki duk da ruwan saman da ake yi.

Kara karanta wannan

An Nadawa Jarumar TikTok Murja Kunya Dukan Kawo Wuka a Kano

Matashi ya ce ba a dauke wuta ba duk da ruwan sama da aka shafe kwana bakwai ana yi a Turai
“Ana Ruwa Amma Duk Da Haka Akwai Wuta”: Matashi Dan Najeriya Da Ke Turai Ya Cika Da Mamaki Hoto: TikTok/@demopumpin.
Asali: UGC

Ya yi barkwaci cikin raha cewa kada dai taransfomar da ke ba da wutar lantarki a yankin ta lalace.

Dan Najeriya da ke zaune a Birtaniya ya ce an shafe kwana bakwai ana ruwan sama

Mutumin yana magana ne kan abun da ke faruwa a Najeriya saboda da zaran an fara ruwan sama, sai a dauke wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mabiyansa da dama, wadanda ke zaune a Birtaniya ma sun yi tsokaci kan abun da yake fadi. Suma sun ce su kan manta cewa ba a Najeriya suke ba yanzu sannan su dunga tunanin za a dauke wuta idan ana ruwan sama.

Shafin @demopumpin ne ya wallafa bidiyon mai ban dariya.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da TikTok sun yi martani ga bidiyon

@Honey_suckle ta ce:

"Wannan ni ce a makon jiya. Ina kallon wani fim sai aka fara ruwan sama. Na fadi a zuciyata, yanzun nan za su dauke wuta."

Kara karanta wannan

Budurwa 'Yar Najeriya Ta Shiga Bakin Ciki Bayan Siyar Da Wayarta Don Saurayinta, Bidiyon Ya Yadu

@Micheal Davidson ya ce:

"Kwarai kuwa! Yanayin akwai sanyi sosai da iska ma."

@desire ya ce:

"Haka abun yake a nan Sweden. Ban fahimci wannan lokacin na rani ba kwata-kwata."

Legit Hausa ta nemi jin yadda abun yake daga bangaren wasu yan Najeriya inda suka ce su kan shiga zullumi a duk lokacin da hadari ya hadu.

Malama Khadija mazauniyar garin Minna ta ce da zaran an dan yi iska ba ruwan sama ba su kan nemi wuta su rasa.

Ta ce:

"Lallai sun ji dadinsu a Turai har kwana bakwai ana ruwa amma ace ba a dauke wuta ba. Mu nan tun shekaran jiya da aka yi dan yayyafi bamu ga ruwa ba sai jiya da daddare. Na rasa wannan dalili ace ba dama ayi ruwa sai dai a saura cikin duhu.

A bangarensa Zainab cewa ta yi da ta hango hadari sai fargaba tana mai cewa:

"Ni fa duk sai na shiga zullumi daga na leka na ga hadari. Wasu lokutan ma yan NEPAN basu jira a fara ruwan daga sun ga iska dif sai su dauke wutan. Ko yaushe muma za mu zama kamar Turai? Allah dai ya kyauta."

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

Budurwa ta yi caraf da saurayinta dan tsurut cike da shauki

A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya sakamakon bayyana hotunanta tare da sahibinta wanda ya kasance dan tsurut da shi.

Hotunan da shafin @holyson101 ya wallafa a TikTok ya nuna yadda matashiyar ta daga mutumin sama sai kace wani dan karamin yaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng