An Kama Mutum 5 da Suka Yi Yunkurin Siyar da Jariri Mai Kwanaki 8 a Kan N30m
- An gurfanar da wasu mutum biyar zargin sun yi yunkurin siyar da jariri mai kwanaki takwas kacal a duniya
- An ruwaito yadda alkali ya ba da umarnin tsare wadanda ake zargin tare da bayyana matakin da za a dauka a gaba
- Ba sabon abu bane a samu masu yunkurin salwantar da jarirai a Najeriya a bangarori daban-daban na kasar
Jihar Kano - Wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano da ke Kwana Hudu ta ba da umarnin tsare wasu mutane biyar bisa zarginsu da yunkurin sayar da jariri dan kwanaki takwas a kan kudi N30m.
Wadanda ake zargin su ne; Kabiru Ibrahim Sauna, Musa Ismail, Hadiza Ibrahim, Ismail Musa da Isyaku Lawan, Daily Trust ta ruwaito.
Ana tuhumarsu ne da baiwa wata Hadiza Ibrahim ‘yar unguwar Sabon Gari a karamar hukumar Fagge kwangilar samo musu jariri sabon haihuwa da bai wuce kwana takwas ba a kan za su ba ta kudi N30m.
Yadda ta kaya a gaban alkali
Mai gabatar da kara, Aliyul Abideen, ya karanta tuhume-tuhumen da ake yiwa wadannan mutane biyar a gaban alkali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, wadanda ake karan na daya da na biyu sun musanta aikata laifin, yayin da na uku da na hudu da na biyar suka amsa laifin da ake tuhumarsu a kai.
Mai gabatar da kara ya roki kotun da ta sanya ranar da za ta yanke hukunci ga wadanda ake tuhumar da suka amsa laifinsu.
Khadi Malam Nura Yusuf Ahmad, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Oktoba.
Son yara ya sa na saci jariri
A wani labarin, wata mata mai suna Mis Diyal yar shekaru 32 ta fadi dalilin da ya sanya ta satar jariri dan kwana uku da haihuwa a Asibitin Kwararrun Filato dake Jos.
Mis Diyal ta bayyana cewa tsananin son gan nin ta samu da wanda zai rika kiranta da sunan uwa ne ya sanya ta satar wannan jariri.
Matar wacce ke karatu a Kwalejin koyar da ilimin kiwon lafiya dake Zawan a Filato, ta yi wannan bayanin ne ga manema labarai ranar Alhamis bayan da ta riga ta shiga hannun hukumar ‘yan sanda.
Asali: Legit.ng