Babbar magana: Ni ciwon da nake yi na satar jarirai ne - In ji matar da aka kama da jariri
- An kama wata mata a garin Ibadan dake jihar Oyo ta saci yarinya 'yar shekara uku
- Matar ta bayyana cewa tana da wani ciwo da yake sanyata tana daukar yara a duk inda ta gansu
- Matar kuma ta amsa laifinta na satar yarinyar inda ta baiwa hukuma hakuri
Wata mata da aka kama da lifin satar jarirai mai suna Oluwatoyin Lasisi, ta dora alhakin wannan laifi nata akan wani ciwo da take fama dashi shekara da shekaru.
Matar wacce take ofishin 'yan sanda na jihar Oyo, an kama ta da laifin sace yarinya 'yar shekara uku mai suna Nimotallah Sulaiman, a yankin da Musulmai suke zama a garin Ibadan na jihar Oyo, matar ta bayyana cewa ba ta san ainahin lokacin da ta dauki yarinyar ba a cikin wata bola ta tafi da ita gidanta ba.
Da take magana akan dalilin da ya saka ta saci yarinyar, matar ta ce: "Ina kan hanyata ta zuwa wajen da nake bara, sai naga karamar yarinyar, sai nayi tunanin bai kamata ba ace na bar ta matsafa su zo su dauke ta su tafi da ita ba, kawai sai na dauke ta.
"Ban san lokacin dana goya ta a bayana ba na tafi da ita gidana. Dana isa gida makociya ta tana tambayata inda na samo yarinya. Sai nake gaya mata yarinyar dan uwana ce da suka samu matsala da matar shi. Da ta fara damuna sai na gaya mata zan dauke ta na mayar da ita wajen iyayenta a daren wannan ranar.
KU KARANTA: Tashin hankali guda biyar da baza a taba mantawa dasu ba har abada a masana'antar Kannywood
"Ina kan hanyar zuwa ofishin 'yan sanda sai wasu mutane suka tsayar dani suka fara dukana, suka kawo ni ofishin 'yan sanda."
Mahaifin yarinyar, Sulaiman Dauda, ya ce matar ta sace yarinyar ne a wajen wata bola inda taje domin tayi bayan gida.
"Ta sanar da mahaifiyarta cewa za tayi bayan gida, sai ta dauketa ta kai ta wajen bolar ba nisa da shagonta, daga nan ne wannan matar ta dauketa," in ji Dauda.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Shina Olukolu, ya sanarwa da manema labarai cewa matar ta amsa laifinta na cewar ta saci yarinyar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng