Tsantsar son haihuwa ne ya sanya ni sata, inji barauniyar jaririn Jos
-Barauniyar jaririn Jos ta bayyana dalilin da ya sanya ta yin satar jaririn
-Mis Diyal wacce ke da shekaru 32 ta ce matukar son haihuwa ne ya sanya ta sace jaririn wata mata amma ba wai da wata manufa ta daban ta aikata wannan laifin ba
Wata mata mai suna Mis Diyal yar shekaru 32 ta fadi dalilin da ya sanya ta satar jariri dan kwana uku da haihuwa a Asibitin Kwararrun Filato dake Jos.
Mis Diyal ta bayyana cewa tsananin son gan nin ta samu da wanda zai rika kiranta da sunan uwa ne ya sanya ta satar wannan jariri.
KU KARANTA:Tirkashi: Dumu-dumu na iske mahaifiyata na zina da limamin mu a cikin gidanmu - Wata budurwa ta koka
Matar wacce ke karatu a Kwalejin koyar da ilimin kiwon lafiya dake Zawan a Filato, ta yi wannan bayanin ne ga manema labarai ranar Alhamis bayan da ta riga ta shiga hannun hukumar ‘yan sanda.
Kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wannan jaririn da matar ta sace, da ne ga wata mata mai suna Mary. Kuma an sace shi ne bayan kwana uku kacal da haihuwarsa a nan Asibitin Kwararrun Filato.
Samun labarin satar wannan jariri wurin ‘yan sanda keda wuya sai suka shiga gudunar da bincike nan take ba tare da bata lokaci ba, inda suka samu nasarar damke matar da ake zargin.
Har wa yau, NAN ta sake bayyana mana cewa matar tayi ikirarin cewa ta taba haihuwa lokacin da masu garkuwa da mutane suka tsare ta. Matar ta sake fadin cewa tana da rajista da sashen kula da mata masu juna biyu na Asibitin koyarwa na Jami’ar Jos.
“ Na kai shekaru 7 yanzu da yin aure, amma ban taba samun haihuwa ba. Wannan shi ne dalilin da ya sanya ni daukar jaririn da ba nawa ba. Mun dade muna neman maganin haihuwa ni da mijina amma har yau bamu samu rabo ba. Ina rokon a taimaka a duba dalilina na satar a kuma sassauta min hukunci na.” Inji ita matar.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng