Shehu Sani Ya Fadi Yadda Ma Su Mulki Ke Karar Da Shekaru 4 A Kan Mulki

Shehu Sani Ya Fadi Yadda Ma Su Mulki Ke Karar Da Shekaru 4 A Kan Mulki

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan siyasa ke karar da shekaru hudunsu a mulki
  • Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Alhamis 28 ga watan Satumba inda ya ce shekara ta farko zuwa kotu kawai ake
  • Ya kara da cewa a shekara ta biyu ne ake kwatanta mulki kadai yayin da shekara ta uku da hudu duka labarin zabe ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan siyasa ke salwantar da shekaru hudu na mulkinsu.

Sani ya ce shekarar farko ta zuwa kotu ce da tabbatar da zabe wanda hakan ya zama ruwan dare, Legit ta tattaro.

Shehu Sani ya fadi yadda su ke karar da shekaru 4 a mulki
Shehu Sani Ya Yi Martani Kan 'Yan Siyasa. Hoto: Shehu Sani.
Asali: Facebook

Akan meye Shehu Sani ya yi magana?

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Alhamis 28 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

An Shiga Ruɗani Kan Hukuncin Kotun Kaduna, Gwamna Uba Sani Ya Maida Martani

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ya ce shekara ta biyu ce ake gudanar da mulki a ofishin gwamnati daban-daban na 'yan siyasa.

Ya kara da cewa shekara ta uku anan ake yin zaben fidda gwani da kuma taron jam'iyya ta kasa.

Sani ya ce yayin da shekara ta hudu ta ke a matsayin shekarar gudanar da babban zaben don sake darewa madafun iko.

Meye Shehu Sani ke cewa kan 'yan siyasa?

Ya ce:

"Yadda mu ke yin shekaru hudu na mulki:
"Shekarar farko ta zabe ce da zuwa kotu.
"Shekara ta biyu ita ce ta mulki.
"Shekara ta uku ta taron jam'iyyu a kasa da kuma zaben fidda gwani.
"Shekara ta hudu ita ake kira shekarar babban zabe."

Sanatan ya bayyana haka ne yayin da ake cikin shari'ar zabe a kasar daban-daban a kotunan zabe.

Kara karanta wannan

Rundunar Tsaro Ta Bayyana Dalili 1 Tak Da Ke Hana Su Kawo Karshen Rashin Tsaro, Ta Yi Bayani

A watan Satumba da mu ke ciki ne aka yanke hukunci tsakanin Tinubu da Atiku da kuma Peter Obi kan zaben shugaban kasa.

Shehu Sani ya fadi wadanda ya kamata Tinubu ya nada minista

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya bayyana wadanda Bola Tinubu ya kamata ya nada mukamin minista.

Sani wanda jigo ne a jam'iyyar PDP ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 27 ga watan Agusta inda ya ce ya kamata Tinubu ya bi kwarewa da kuma iya aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.