Bayan Shafe Fiye Da Shekaru 10 a Amurka, Attajiran Mata Ta Talauce, Ta Koka a Bidiyo

Bayan Shafe Fiye Da Shekaru 10 a Amurka, Attajiran Mata Ta Talauce, Ta Koka a Bidiyo

  • Wata mata ta ba da labarinta mai karya zuciya, tana mai bayyana yadda ta tashi daga attajira zuwa mara komai
  • Attajiran matar ta zauna kasar Amurka tsawon shekaru fiye da 10 kuma ta mallaki miliyoyi da motoci biyu
  • Abun takaici, ta koma gida a Afrika sannan abubuwa suka tabarbare tun bayan barinta Amurka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mata mai suna Beatrice Jockey Mangure ta roki jama'a da su taimaka mata da kudi don ta magance matsalar idonta da kuma fara sana'ar tasi.

Afrimax ya yi hira tare da wallafa labarin Beatrice don sanar da duniya halin da take ciki da nema mata taimako.

Beatrice ta kasance attajira kafin ibtila'i ya saukan mata
Bayan Shafe Fiye Da Shekaru 10 a Amurka, Attajiran Mata Ta Talauce, Ta Koka a Bidiyo Hoto: Afrimax English
Asali: Youtube

Beatrice ta kasance attajiran mata

A cewar Beatrice, mutuniyar kasar Kenya, ta yanke shawarar komawa Amurka ne bayan aurenta na shekaru shida ya mutu. Matar mai yara biyu ta je kasar Amurka sannan ta ya da zango a Georgia sannan ta fara neman na kai ta sana'ar girkinta.

Kara karanta wannan

Rudani: An kwato gawar wata mata daga bakin kada, jama'a sun shiga jimami

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kasuwancinta ya bunkasa ta yadda har ta iya mallakar gida mai kyau. Yayin da take bayyana cewa rayuwar Amurka ba sauki, kuma cewa ta yi fama da lalurar damuwa saboda mutuwar aurenta, Beatrice ta ce tana samun miliyoyi a chan.

Ta mallaki motoci biyu kuma tana da wadata sosai.

Beatrice ta yanke shawarar komawa gida

Bayan ta sha fadi da illata kanta, Beatrice ta ce ta zata shawara mai kyau ta yanke na komawa gida Kenya da zama.

Sai dai kuma, daga nan ne matsalolinta suka fara. Kalamanta:

"Lokacin da na koma Kenya, na dauki gaba daya kayana harma na siya sabbin kaya. Na saka su a kwantena amma na rasa dukka.
"Bai zo Kenya ba ko kadan. Na dawo da akwatuna biyu ne kawai da na zo filin jirgin sama da su. Shine abun da na kawo kasar nan kawai. Na rasa abubuwan kudi da yawa, miliyoyin naira."

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda wata mata ta fito titi neman a taimake ta ta siya iPhone 15

Gaba kasuwancin da ta so farawa bayan ta isa Kenya sun lalace yayin da mutane ke damfararta, Yanzu matar tana samun madogara ne a matsayin direbar tasi, inda take amfani da motar wani da take haya.

Kalli bidiyon a kasa:

Labarin Beatrice Jockey Mangure ya tsuma zukata

@beautyadaarewa638 ta ce:

"Nagode sosai da kika ba da labarinki. Ya sa na koyi darasi, don na tsara rayuwata kafin na rasa madogara, saboda idan kana matashi, kana da karfi da kwarinka, yayin da kake tsufa karfin na raguwa."

@frankie6207 ta ce:

"Wannan labari mara dadi ne kuma darasi garemu mu dukka da ke zaure a Turai. Mu kasance da hannun jari saboda gaba. Kada mazauna waje su yarda sosai da yan uwa da abokai kan su taimaka masu da abun da ya shadi kudi. Allah zai kawo mata mataimaki ta shirin Lynn Ngugi."

@yvonnemascoll356 ta ce:

"Ina rokon Allah ya juyo da lokaci sannan cewa matar nan za ta samu wadata ta dukiya, lafioya da kwakwalwa a kowani bangare na rayuwarta. Allah ya sani ta cancance shi...."

Kara karanta wannan

Hotunan Wani Katafaren Gida Da Za a Siyar Miliyan 1.5 Ya Girgiza Intanet

Matashiya da ta auri dattijo ta nunawa duniya shi a bidiyo

A wani labari na daban, wata matashiya yar Najeriya wacce ta aure wani dattijo ta haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya yayin da ta baje kolin mijinta.

Matashiyar, @asmawu.hamisu, ta kira dattijon da "rayuwata" sannan ta rike hannunsa a kan teburin cin abinci yayin da suke bidiyon a TikTok.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng