Dan Najeriya Ya Shiga Dimuwa, Bayan Gano Attajirin Makwabcinsa Na Kwanciya Da Matarsa, Bidiyon Ya Yadu

Dan Najeriya Ya Shiga Dimuwa, Bayan Gano Attajirin Makwabcinsa Na Kwanciya Da Matarsa, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani matashi ya shiga dimuwa bayan ya gane matarsa tana zuwa wurin makwabcinsa mai kudi don cin amana
  • A cikin wani faifan bidiyo daya wallafa, Postsubman cikin kuka da bacin rai ya ce makwabcin nasa yana cin amanarsa
  • Ya yi alkawarin daukar mataki akan makwabcin da kuma matar tasa, inda mutane da dama suka mai da martani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani dan Najeriya ya bayyana yadda makwabcinsa ke cin amanarsa bayan ya gano matarsa na kai masa ziyara.

A wani faifan bidiyo da ya wallafa yana kuka, Postsubman ya ce matarsa tana kwanciya da makwabcinsa mai kudi, cewar Legit.ng.

Matashi ya shiga dimuwa bayan gano makwabcinsa na kwanciya da matarsa
Bidiyon Dan Najeriya Bayan Gano Attajirin Makwabcinsa Na Kwanciya Da Matarsa. Hoto: @Postsubman.
Asali: Twitter

Matashin wanda yake ta masifa a cikin yaren Yarbanci ya bukaci makwabcin mai suna Baba Collins ya fito masa da matarsa.

Ya yi alkwarin daukar mummunan mataki akan makwabcin da matar tasa inda ya ce ba zai hakura ba.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Shiga Yanayi Bayan Saurayinta Ya Gudu Saboda An Yanke Mata Kafa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Faifan bidiyon ya jawo kace-nace a tsakanin mutane.

Kalli faifan bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun maida martani kan bidiyon da matashin ya wallafa:

@Brhoelyfather:

"Matar ya kamata ta bar yankin ko da kuwa ba ta cin amana, saboda bacin ran mutumin nan yafi na shedan, zai iya yin komai, ya kamata mu guji kula matan mutane."

@ceowilikconcept:

"Kai, na taba fuskantar haka, babu dadi, tsohuwar budurwata ta lalata min tunani, kawai na maida komai na ga ubangiji, rayuwa ta yanzu ta yi, duk da na sha wahala a baya."

@Gidi_lawd:

"Na so na yi dariya, amma na tuna yadda David a Injila ya dauki matar wani, ubangiji ya turo annabi Nathan don masa magana, abin da wannan mai kudi ya yi wa talakan nan shaidanci ne."

@FamousCole_AO:

"Wannan tabbas ba wasa ba ne, da kyar yake numfashi, zai iya tarwatsa komai."

Kara karanta wannan

“Uwar Miji Ta Ce Ba Zan Taba Haihuwa Ba”: Yar Najeriya Ta Samu Cikin Yan 3, Ta Nuna Wa Duniya

@urchmonniie:

"Ya kori matar kawai, ba a fada da masu kudi. Za su yi amfani da kudi su juya ka, kawai ka barta ta tafi ka ci gaba da rayuwarka."

@CUdoaku:

"Irin wannan mutum zai yi wahala ya fito daga gidan."

@josh__tntl:

"Abin bakin ciki, daga muryarsa zaka gane yana cikin bacin rai, babu abin da ke da tabbas a rayuwa."

Budurwa Ta Rufe Fuskarta Don Kunya Bayan Ta Yi Wa Kawayenta Karya A Otal

A wani labarin, wata budurwa ta sha kunya bayan haduwa da kawayenta a cikin wani otal.

Budurwar ta taba yi wa kawayen karya cewa ita ce mai tarbar baki a otal din, kwatsam sai suka ci karo da ita.

Sun gano cewa ashe ita mai gadi ce a otal din, nan da nan suka fara nadar bidiyonta yayin da ita kuma ta tsere da gudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel