Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Jam'iyyar ADC Kan Gwamnan Jihar Gombe

Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Jam'iyyar ADC Kan Gwamnan Jihar Gombe

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Gombe, ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta shigar kan zaɓen gwamna
  • Jam'iyyar ta shigar da ƙara ne a gaban kotun domin ƙaƙubalantar nasarar da gwamnan Inuwa YahAya da mataimakinsa suka samu a zaɓen 2023
  • Kotun ta yi watsi da ƙarar inda ta bayyana cewa jam'iyyar ta kasa kawo ingantattun hujjoji na zargin an tafka maguɗi a zaɓen

Jihar Gombe - Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Gombe da ke zamanta a Gombe, a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) kan zaɓen gwamnan jihar.

Jam'iyyar ADC ta shigar da ƙara a gaban kotun ne domin ƙin amincewa da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya da mataimakinsa, Manasseh Jatau a zaɓen gwamnan jihar na 2023.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Kotu ta yi watsi da karar ADC kan gwamna Inuwa Yahaya
Kotu ta yi fatali da karar jam'iyyar ADC kan nasarar gwamna Inuwa Yahaya Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Jam'iyyar ADC ta shigar da ƙarar ne inda take zargin akwai saɓani a cikin sunayen takardun shaidar karatu da mataimakin gwamnan ya mika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin zaɓen ranar 18 ga watan Maris.

Sai dai kotun wacce mai shari’a S.B Belgore, yake jagoranta ta yi watsi da ƙarar, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotun ta yi fatali da ƙarar?

Alƙalin kotun ya ce ƙorafin na jam'iyyar abu ne wanda ya shafi kafin zaɓe, inda ya ƙara da cewa Jatau yana da mafi ƙarancin abin da ake buƙata na tsayawa takarar kujerar mataimakin gwamna, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kotun ta kuma yi fatali da zarge-zargen da ADC ta yi na tafka kura-kurai da sayen kuri’u a lokacin zaɓen gwamnan saboda rashin hujjoji.

A halin yanzu, Kotun ta na yanke hukunci kan ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna suka shigar kan zaɓen.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Hasashen Wanda Zai Yi Nasara Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Legas

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Sanwo-Olu

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas, ta yi fatalo da ƙararrakin jam'iyyun PDP da Labour Party kan nasarar gwamna Sanwo-Olu na jam'iyyar APC.

Kotun ta tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng