Yadda Aka Bindige Wani Mutum Yayin Da Ya Tafi Sace Makwabcinsa A Neja
- Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki gidan Wakilin Nufawa, Alhaji Mohammed Makasudi a jihar Neja
- 'Yan bindigan guda shida sun durfafi gidan mutumin inda su ka kwashi kashinsu a hannu
- Daya daga cikin 'yan bindigan daya samu harbi a kafa ya kasance makwabcin mutumin ne
Jihar Neja - Wani matashi ya hadu da tsautsayi yayin da yi niyyar yin garkuwa da makwabcinshi a jihar Neja.
Matashin mai suna Isma'ila ya hadu da harbin bindiga inda ya tara gungun masu garkuwan don sace makwabcinshi.
A ina 'yan bindigan su ka kai hari a Neja?
'Yan bindigan sun kai farmakin ne gidan Alhaji Mohammed Makasudi da ke Sabon Wuse da ke karamar hukumar Tafa da ke jihar, cewar Daily Trust.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a
Wani makwabcin mutumin ya bayyana yadda Alhaji Mohammed ya harbe 'yan bindigan wanda daga bisani ya fahimci har da makwabcinshi.
Ya ce:
"Lokacin da 'yan bindigan su ke ta harbe-harbe, Wakilin Nufawa ya bukaci a bude musu kofa yayin da ya ke rike da bindiga.
"Ya na bude kofar sai ya harbi daya daga cikinsu inda ya mutu nan take.
"Ya sake harba bindigar sai ya samu daya a kafa inda ya fahimci makwabcinshi ne na kusa."
Wane martani 'yan sanda su ka yi a Neja?
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce jami'an tsaro sun bindige 'yan bindigan.
Ya ce a ranar Asabar 23 ga watan Satumba da misalin karfe 11 na dare 'yan bindiga guda shida sun durfafi Sabon Wuse inda 'yan sanda su ka yi artabu da su.
Ya ce:
"Yayin artabun, daya daga cikinsu ya rasa ransa, yayin da wani daga cikinku ya samu rauni wanda aka bayyana da Isma'ila Abdullahi mai shekaru 20."
Ya kara da cewa sauran 'yan bindigan sun tsere cikin daji da raunuka a jikinsu, Arewa maso Tsakiya na fama da hare-haren 'yan bindiga musamman a yankunan karkara, Anadolu Ajansi ta tattaro.
Ba zan sake jiran Tinubu ba kan ayyuka, Umar Bago
A wani labarin, Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya ce ba zai sake jiran Shugaba Tinubu ba wurin gyara hanyoyi a jihar.
Gwamnan ya ce zai ci gaba da gyara hanyoyin idan yaso daga baya ya yi lissafin abin da ya kashe a biya shi musamman yadda hanyoyin jihar su ka lalace.
Asali: Legit.ng