Mai Adaidaita Ya Tsinci Wayar iphone 14 Pro Max Da Fasinja Ya Manta, Ya Mayarwa Mai Ita

Mai Adaidaita Ya Tsinci Wayar iphone 14 Pro Max Da Fasinja Ya Manta, Ya Mayarwa Mai Ita

  • Wani matashi mai adaidaita sahu ya yi fice bayan ya mayar da wayar iphone 14 Pro Max da fasinjansa ya manta
  • Saboda wannan karamci nasa, mai wayar ya yi masa kyautar kudi ¢300 (N20,128.82)
  • Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi na bidiyon suna masu jinjinawa matashin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan kasar Ghana wanda ke aiki a matsayin dan adaidaita a Kumasi ya sha jinjina saboda kamanta gaskiya bayan ya mayar da wayar wani fasinja.

Fasinjan wanda ya cika da farin ciki, ya yaba da gaskiyar matashin sannan ya yanke shawarar jinjina masa, yana mai bayyana cewa ya shiga damuwa bayan ya gane cewa ya baro wayarsa iPhone 14 Pro Max a adaidaitan.

An bai wa dan adaidaita tukwici
Mai Adaidaita Ya Tsinci Wayar iphone 14 Pro Max a Kekensa, Ya Mayarwa Mai Ita Hoto: @gyenyame4ever/TikTok
Asali: TikTok

An gano iphone 14 Pro Max da ya bata

Ya ce a lokacin da ya kira lambarsa, mai adaidaitan ya yarda su hade domin ya karbi wayar tasa ba tare da jinkiri ba.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fashe Da Kuka Wiwi Yayin da Saurayi Ya Yi Mata Korar Kare Daga Gidansa a Bidiyo

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dan adaidaitan, wanda ya tsaya hankali kwance yayin da ake jinjina masa, ya ce abu na farko da ya fara zuwa zuciyarsa a lokacin da ya wayar a cikin adaidaitansa shine ya gano mai ita sannan ya mayar da ita sumul kalau.

Dan adaidaita ya yi wa fasinja godiya

Saboda gaskiyar da ya nuna a kan aikinsa, fasinjan ya yi masa kyautar kudi ¢300 (N20,128.82) a matsayin tukwici.

"Ina so na gode maka a kan wannan kyauta. Na sha mayar da kayayyakin da na tsinta a adaidaitana ga masu shi, da yawansu basu bani kudi ba, kuma wasu basu ma ce sun gode ba. Ina mai godiya ga wannan," cewarsa dauke da murmushi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yaba ma mai adaidaita mai gaskiya

Jama'a da suka ga bidiyon sun jinjinawa matashin saboda gaskiyar da ya nuna a kan aikinsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mawaki Rarara Ya Gamu Da Tsautsayi Na Hatsarin Mota, Bayanai Sun Fito

Puzor Junior ya bayyana cewa:

"Na tsinci wayar Samsung S20 ultra a motar tasi na. Wayar na tare da ni tsawon kwana 3. Bayan na ba shi wayar har so ya yi ya kama ni."

_ stated:

"Saboda tsarkakakkiyar zuciyarka ba za ka taba rashi ba a rayuwarka har abada."

S A I F indicated:

"Wadannan yan adaidaitan a Kumasi suna da kirki gaskiya...bayin Allah ne."

An yi wa matashin mai a-daidaita-sahun da ya dawo da N15m tayin yan mata 4 da zai aura

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Auwalu Salisu, direban a-daidaita-sahun da ya mayarwa ɗan ƙasar Chadi naira miliyan 15, an yi masa tayin ƴan mata huɗu da zai aura.

Ƙungiyar haɗa aure ta Kano wacce aka fi sani da Mai Dalilin Aure, ta ce Salisu zai zaɓi ƴan mata huɗu daga cikin 10 da za a ba shi, cewar rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng