“Ya Tsorata”: Martanin Jama’a Bayan Dan Adaidaita Ya Mayar Da Miliyan 15 Da Fasinja Ya Manta Da Shi

“Ya Tsorata”: Martanin Jama’a Bayan Dan Adaidaita Ya Mayar Da Miliyan 15 Da Fasinja Ya Manta Da Shi

  • Wani dan adaidaita mai shekaru 22 ya burge yan Najeriya bayan ya mayar da makudan kudaden da wani fasinja ya manta a kekensa
  • Fasinjan wanda ya zo daga kasar Chadi don siyan kayayyaki a Kano ya manta da baira miliyan 15 a adaidaita sahun matashin
  • Nan take dan adaidaitan ya mayar da kudin bayan ya samu sakon sanarwa kan batan kudin a radiyo

Wani direban adaidaita sahu dan shekaru 22 mai suna Auwalu Salisu ya mayar da kudi naira miliyan 15 da fasinjansa ya manta a jihar Kano.

A cewarsa, ya mayar da kudin ne bayan ya samu wata sanarwa game da batan kudin a radiyo a Kano.

Dan adaidaita ya mayarwa fasinja da kudin da ya manta
“Ya Tsorata”: Martanin Jama’a Bayan Dan Adaidaita Ya Mayar Da Miliyan 15 Da Fasinja Ya Manta Da Shi
Asali: Instagram

Salisu ya mayar da tsabar kudi naira miliyan 15

Tsabar kudin ya kai naira miliyan 15 idan canja saifar 10.130 million CFA da naira miliyan 2.9.

Kara karanta wannan

"Sabuwa Fil a Leda": Ango Ya Nuna Zumudinsa Bayan Ganin Fuskar Amaryarsa a Daren Farko, Bidiyon Ya Yadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake tattaunawa da Radiyon Arewa Radio da ke Kano, matashin ya bayyana cewa bai lura cewa fasinjansa ya manta da kudin ba har sai da ya isa gida.

Wani hoto da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno dan adaidaitan rike da kwalin kudin da ya mayar.

Martanin jama'a yayin da dan adaidaita ya mayar da miliyan 15

Wallafar ya janyo martani da dama daga jama'a wadanda suka jinjinawa amanar direban adaidaitan sannan sun nuna fatan cewa za a basa tukwicin wannan karamcin nasa.

@sleekey9.0 ya ce:

"Ta yaya kake iya yawo hankali kwance da irin wannan makudan kudaden? Kuna da zuciya faaa, idan na dauki 100k kawai a jaka, na kan fi iska gudu saboda duk wanda ke kusa dani abun zargi ne."

Kara karanta wannan

Yadda Dakarun Sojoji Suka Kama Makashin Dorathy Jonathan a Kudancin Kaduna

@the_hunteezz ta kara da cewar:

"Manta, akwai mutanen kirki a kowani hali."

@lymdafelix:

"Mutum na da zuciyar mantawa da miliyan 15. Bari na rasa kamar #100 haka, ina iya bayyana a gidan talbijin din NTA domin yadda zan nemi #100 koooh."

@unlimited_cash007 ta yi martani:

"Don Allah ku yi binciken sunaye da kyau kafin sanyawa yaranku yana da matukar muhimmanci."

@onyeka.gram ya ce:

"An yi masa asiri ne."

@jesseblinkz_ ta rubuta:

"Tsoro ne ya kama shi ya mayar da shi."

@yhulukluvly ya ce:

"Wasu mutanen sun iya manta abu fa. Har miliyan 15? Bana manta canjin naira 50 ma."

@shedsntdomakeup1 ta ce:

"Mutanen kirki na nan har yanzu."

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Lagas

A wani labari na daban, mun ji cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka zuba a safiyar Asabar, 16 ga watan Satumba ya yi sanadiyar ambaliyar ruwa da ta yi barna a unguwannin jihar Lagas.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, yankunan da abun ya shafa sun hada da hanyuar LASU-Igando, babban titin Lagas-Badagry, da suaran yankunan Lagas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng