Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Koma Jami'ar Tarayya Ta Gusau, Sun Sace Ma'aikatan Gini

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Koma Jami'ar Tarayya Ta Gusau, Sun Sace Ma'aikatan Gini

  • Bayan sace ɗalibai mata, 'yan bindiga sun yi awon gaba da masu aikin gini da yawa a jami'ar tarayya da ke Gusau
  • Ɗaya daga cikin ma'aikatan, Ibrahim Muhammad, ya ce maharan sun shiga ginin da suke kwana, suka kwashi akalla mutane 9
  • Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan samun labarin 'yan bindiga sun sace ɗalibai mata a ɗakunan kwanansu ranar Jumu'a

Jihar Zamfara - Miyagun ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da wasu ma’aikatan gini guda tara a jami’ar tarayya ta Gusau da ke jihar Zamfara.

Da yake zantawa da jaridar Punch, ɗaya daga cikin ma’aikatan da ya bayyana sunansa da Ibrahim Mohammed, ya tabbatar da sace abokan aikinsa.

Harin yan bindiga a jami'ar Gusau.
Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Koma Jami'ar Tarayya Ta Gusau, Sun Sace Ma'aikatan Gini Hoto: punchng
Asali: UGC

Ya ce ‘yan bindigan haye a kan babura, sun shiga jami’ar ne da sanyin safiyar ranar Juma’a, 22 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Miyagu Sun Buɗe Wuta Yayin da Suka Kai Mummunan Hari Gidan Babban Jigon Siyasa a Arewa, Sun Tafka Ɓarna

Yadda yan bindiga suka sace ma'aikatan gini

Mutumin ya bayyana cewa daga zuwan 'yan ta'addan, nan take suka kutsa cikin ginin da ma'aikatan ke kwanciya su yi bacci, suka tattara su suka yi awon gaba da su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Malam Muhammad ya yi bayanin cewa ya samu nasarar iya tsallakawa ta taga, ya arce da gudun tsiya domin tsira daga nufin 'yan bindigan.

A kalamansa ya ce:

"Lokacin da suka shigo cikin ginin da muke kwance, sun faɗa mana mu tashi mu fito daga wurin mu bi su. Nan na fara waige-waigen neman hanyar guduwa."
"Ba su yi tsammani ba na yi tsalle na haura ta taga, ɗaya daga cikin 'yan bindigan ya harbo harsashi amma Allah ya tsare bai same ni ba.

Duk wani yunƙuri na jin ta bakin mahukuntan jami'ar tarayya ta Gusau kan wannan harin bai kai ga nasara ba, kamar yadda This Day ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Sai dai jami'in tsaron makarantar da ya nemi kada a ambaci sunansa, ya shaida wa jaridar cewa ba su da hurumin yin magana kan lamarin.

"Da fatan za a yi haƙuri da mu. Ina daya daga cikin jami'an tsaro na wannan jami'a. Kun san abin da ya faru dangane da sace dalibanmu da ma’aikatan gini."

Yan Daba Sun Farmaki Jigon SDP a Jihar Kogi, Sun Banka Wa Motarsa Wuta

A wani rahoton kun ji cewa 'yan daba sun kai hari gidan wani jigon jam'iyyar SDP a jihar Kogi yayin da ake tunkarar zaben gwamna a watan Nuwamba.

Maharan sun buɗe wuta kan mai uwa da wani kana suka ƙona motocin da suka taras a gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262