Cardoso Ya Fara Aiki a Matsayin Sabon Mukaddashin Gwamnan CBN

Cardoso Ya Fara Aiki a Matsayin Sabon Mukaddashin Gwamnan CBN

  • Sabon mukaddashin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya shiga Ofis a karon farko ranar Jumu'a 22 ga watan Satumba, 2023
  • Mista Olayemi Michael Cardoso, ya karɓi rantsuwar kama aiki tare da mataimakan gwamna 4 a hedkwatar CBN da ke Abuja
  • Wannan na zuwa ne bayan Emefiele da sauran abokan aikinsa sun yi murabus daga kujerunsu na CBN

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - A hukumance, Mista Olayemi Michael Cardoso, ya kama aiki a matsayin sabon muƙaddashin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Mista Cardoso ya hau wannan matsayin ne biyo bayan naɗin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya masa, gabanin majalisar dattawa ta tantance shi.

Sabon mukaddashin gwamnan CBN, Olayemi Michael Cardoso.
Cardoso Ya Fara Aiki a Matsayin Sabon Mukaddashin Gwamnan CBN Hoto: Dailytrust
Asali: UGC

Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye a babban banki CBN bayan Mista Godwin Emefiele, ya yi murabus daga kujerar gwamnan babban bankin Najeriya.

Daraktan sadarwa na CBN, Isa AbdulMumin, shi ne ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu ranar Jumu'a, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP Ta Yi Sabon Canji Bayan Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida a Jihar Kano

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka nan ya ce mataimakan gwamnan da aka naɗa sun shiga Ofis a matsayin riƙo biyo bayan murabus ɗin Folashodun Shonubi, Aishah Ahmad, Edward Lametek Adamu, daga Kingsley Obiora da matsayin mataimakan gwamnan CBN.

Sabon gwamnan CBN, Mista Cardoso, da sauran abokan aikinsa huɗu sun shiga Ofis ne bayan karɓan ranstuwar kama aiki a wani biki da aka shirya a hedkwatar CBN da ke Abuja.

A halin yanzu su ke da alhakin gudanar da duk wasu tsare-tsare da manufofin kuɗi amadadin gwamnatin tarayyan Najeriya.

Takaitaccen tarihin sabon gwamnan CBN

Cardoso yana da gogewa sosai, kasancewar ya riƙe mai ba da shawara kan harkokin tattalin arziki da ci gaba, shugaban sashen kudi, tsohon shugaban kamfanin Citi Nigeria.

Daily Trust ta tattaro cewa bayan haka kuma Cardoso ya kasance tsohon kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziƙi da kasafin kuɗi a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ƙara Tankaɗe da Rairaya, Ya Kori Wasu Manyan Ma'aikata

Ya yi digiri a na farko a Jami'ar Aston da ke Burtaniya da kuma digiri na biyu a Harvard Kennedy School da ke Amurka.

Gwamnatin Kebbi Ya Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai

A wani rahoton na daban Gwamnatin Nasiru Idris ta jihar Kebbi ta haramta ayyukan haƙo ma'adanai a faɗin jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya

Sakataren gwamnatin Kebbi, Yakubu Tafida, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda yanayin taɓarbarewar tsaro a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262