Wike Ya Kwace Filayen Wasu Tsoffin Gwamnonin PDP a Abuja
Akalla tsoffin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) uku ne suka rasa kadarorinsu, yayin da hukumar babban birnin tarayya (FCTA) a karkashin jagorancin Nyesom Wike ta kwace filayensu.
A ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba ne hukumar FCTA ta bayar da umurnin kwace filayen a cikin wata sanarwa da aka buga a jaridu, tana mai bayyana cewar an soke su ne saboda sun ki bunkasa filayen ko kuma saba doka a babban birnin tarayya.
A lokacin da ya kama aiki a matsayin ministan babban birnin tarayya, Wike ya sha alwashin soke duk wani fili da ya saba dokar amfani da filaye ta Abuja, ba tare da la’akari da wanda abin ya shafa ba.
Daga cikin mutane da kungiyoyi 168 da abun ya shafa harda tsoffin gwamnoni uku da suka yi mulki a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
Ga jerin sunayen tsoffin gwamnonin a kasa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Peter Obi
Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, yana daya daga cikin wadanda umurnin soke filayensu da FCTA ta bayar ya shafa.
Kafin ya koma jam'iyyar Labour Party, Obi ya kasance gwamnan jihar Anambra sau biyu a karkashin PDP. Ya fara a matsayin gwamnan jihar karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance a 2006 amma ya kare da PDP a 2014.
2. Liyel Imoke
Ya kasance wani tsohon gwamna wanda ya yi mulki a karkashin PDP kuma yana daga cikin mutanen da Nyesom Wike ya bayar da umurnin soke filayensu.
Imoke ya kasance tsohon gwamnan jihar Cross Rivers tsakanin 2007 da 2016, da shari'o'in kotu a tsakani.
3. Joshua Dariye
Dariye ya yi mulki a matsayin gwamnan jihar Filato karkashin inuwar jam'iyyar PDP tsakanin 2004 da 2007.
An kama shi tare da garkame shi kan wawure kudade. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi masa afuwa.
Wike ya rusa shahararriyar kasuwar kilishi a Abuja
A wani labarin, mun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sake rusa wata shahararriyar kasuwa a Abuja.
A ranar Litinin, 18 ga watan Satumba ne hukumar babban birnin tarayya (FCTA) ta rusa shahararriyar kasuwar Kilishi da ke yankin Area 1 Abuja, jaridar Punch ta rahoto.
Asali: Legit.ng