Sheikh Faskari Ya Shawarci Mutane Su Kare Kansu Daga Harin 'Yan Bindiga A Katsina
- Malamin addinin Musulunci ya shawarci mutane su kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga
- Sheikh Musa Ibrahim Faskari ya bayyana haka ne yayin hudubar sallar Juma'a da aka yada a kafafen sadarwa
- Malamin ya ce Musulunci ya bai wa mabiya addinin damar daukar makami da kare kansu yayin hare-hare
Jihar Katsina - Fitaccen malamin addinin Muslunci a Katsina, Sheikh Musa Ibrahim Faskari ya shawarci mutane su kare kansu.
Faskari ya ba da shawarar ce ga yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da su dauki makamai don kare kansu.
Meye malamin ya ce kan hare-haren 'yan bindiga?
Malamin ya bayyana haka ne yayin gabatar da hudubar sallar Juma'a da aka yada a kafafen sadarwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce addinin Musulunci ya karfafi mabiya addinin da su dauki makamai don kare kansu idan ana kai musu hare-hare.
Ya ce addinin Musulunci ya bai wa Musulmai damar kare kansu daga addininsu da lafiya da dukiya da iyalai da kuma martabarsu.
Ya bayyana yadda aka mayar da mutane bayi
Ya ce:
"Mu na ganin yadda jami'an tsaro ke cike a yankunan mu amma kuma mu na fama da hare-haren 'yan bindiga.
"'Yan uwanmu sun zama bayin wasu a garuruwansu, su na aikin gona a banza, ba za mu yadda da cin zarafi ba.
"Dukkanmu ba ma son mutuwa kuma ba ma kokarin hada kai don kawo karshen abin."
Jihohin Arewa maso Yamma na fama da hare-haren 'yan bindiga a yankuna da dama, Daily Trust ta tattaro.
A daren jiya da misalin karfe 3 na dare 'yan bindiga sun sace daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Gusau.
'Yan bindigan sun kai farmakin ne a dakunan kwanan dalibai uku inda su ka yi awun gaba da dalibai da dama wadanda ba a san yawansu ba.
'Ya sanda sun cafke wani kasurgumin dan bindiga a Katsina
A wani labarin, jami'an tsaro sun cafke wani dan bindiga mai suna Sa'idu Yaro da aka fi sani da Sabon Jini a jihar Katsina.
Wanda aka kaman ana zargin ya kashe kwamandan 'yan sanda a yankin Dutsen-Ma, ACP Aminu Umar.
Asali: Legit.ng