Nasiru Gawuna Ya Ce Baya Tsoron Daukaka Karar Da Gwamna Abba Zai Yi

Nasiru Gawuna Ya Ce Baya Tsoron Daukaka Karar Da Gwamna Abba Zai Yi

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressuves Congress (APC), Nasiru Gawuna ya yi magana kan hukuncin kotun zaɓe
  • Gawuna ya bayyana cewa hukuncin kotun nufi ne na Allah kuma sun karɓe shi da zuciya ɗaya
  • Ɗan takarar ya bayyana cewa baya tsoron ɗaukaka ƙarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce zai yi kan hukuncin kotun

Jihar Kano - Ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Kano na ranar, 18 ha watan Maris, Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa baya jin tsoron ɗaukaka ƙarar da za a yi domin ƙalubalantar nasarar da ya samu a kotun zaɓe.

A ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta tsige gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Ganduje, Gawuna Suka Yi Murna Bayan Kotu Ta Tsige Abba Ya Yadu

Gawuna ba ya tsoron daukaka karar da gwamna Abba zai yi
Nasiru Gawuna ya godewa Allah kan nasarar da ya samu a kotun zabe Hoto: Abba Kabir Yusuf, Journalist KC
Asali: Facebook

Kotun ta zaftare ƙuri'u 165,663 daga cikin na gwamna Abba Kabir a matsayin marasa inganci inda ta bayyana cewa takardun ƙuri'un 165,663 babu tambari ko sannu a jikinsu saboda haka ba su da inganci.

Wane martani Gawuna ya yi kan hukuncin kotu?

Da yake magana kan hukuncin kotun a wata hira da BBC Hausa, Gawuna ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Alhamdulillah mun godewa Allah da ya nuna mana wannan rana (Laraba) da aka yi wannan hukunci wanda kotu ta tabbatar da mu a matsayin waɗanɗa suka ci zaɓe. Ina godiya ga lauyoyinmu da jama'a bisa goyon bayansu da addu'o'i."
"Ko a bayyana an ayyana an ce jam'iyyar NNPP ce ta ci zaɓe, kuma Alhamdulillahi abin da muka ce shi ne Allah shi yake yi babu wanda ke yi kuma mun bar masa hukuncinsa. Sai kuma Allah ya bayar da damar za a iya zuwa kotu domin a nemi haƙƙi, kuma aka je kotun.

Kara karanta wannan

"Akwai Kura-Kurai": Gwamna Abba Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu, Ya Bayyana Mataki Na Gaba Da Zai Dauka

"Wannan hukuncin ma da aka yi Allah ne ya yi, saboda haka babu wani damuwa ga wanda ya yarda da Allah, ya kuma san Allah ke yi, da kuma ƙudirinsa na cewa shi abin da yake so shi ne ya tsarkake zuciyarsa abin da yake so shi ne bautawa al'umma, ba zai taɓa damuwa ya ce ko a mutu ko ayi rai ba a wannan al'amari na mulki.

Gawuna ba ya tsoron gwamna Abba ya dauka ƙara

Da aka tambaye shi ko yana tsoron ɗaukaka ƙarar da gwamna Abba zai yi, sai Gawuna ya kada baki ya ce:

"Duk wanda ya yarda cewa duk abin da ya faru nufi ne na Allah, ba zai taɓa damuwa ko ɗaukar mulki a matsayin a mutu ko ayi rai ba. Duk abin da ya faru da mu, mun yi imani cewa nufi ne na Allah. Ba ma jin tsoro ko fargaba, saboda mun san cewa duk abin da ya faru shi ne daidai domin Allah baya kuskure."

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Kujerar Gwamnan Kano, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaɓe

Ganduje Da Gawuna Sun Yi Murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa da ɗan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar, Nasiru Gawuna, sun yi murna kan nasarar da suka samu a kotu.

Murnar ta su na zuwa ne bayan kotun zaɓen ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel