Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Lagas, NEMA Ta Yi Martani

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Lagas, NEMA Ta Yi Martani

  • Yayin da ake tsaka da fama da ambaliyar ruwa a Lagas, an bukaci mazauna jihar da su dauki matakan kariya
  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta bayar da shawarar a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba
  • Hukumar NEMA ta bayyana cewa za a raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa, kuma ana ci gaba da tattaunawa da al’ummomin da abin ya shafa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka zuba a safiyar Asabar, 16 ga watan Satumba ya yi sanadiyar ambaliyar ruwa da ta yi barna a unguwannin jihar Lagas.

Kamar yadda rahotanni suka kawo, yankunan da abun ya shafa sun hada da hanyuar LASU-Igando, babban titin Lagas-Badagry, da suaran yankunan Lagas.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Lagas
Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Lagas, NEMA Ta Yi Martani Hoto: NEMA Nigeria
Asali: Twitter

Hotuna da bidiyo yi sun bayyana yadu a soshiyal midiya inda aka ga irin barnar da ambaliyar ruwan ta yi.

Kara karanta wannan

Ana zaman dar-dar: Gini ya ruguje kan jama'a, mutum 2 suna can jina-jina a asibiti

NEMA ta yi martani

Da take martani ga ci gaban, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta gargadi maauna yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa a Lagas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wata sanarwa da ta saki a shafinta na X a ranar da abun ya faru, ta bukaci mazauna jihar Lagas da su kara taka-tsan-tsan saboda ci gaban ruwan saman da ya fara da karfe 0200 kuma ake sa ran zai ci gaba har zuwa karfe 13:00."

Hukumar ta ce ta fara aikin duba wuraren tare da tattaunawa da al'umomin da abun ya shafa don ba da mafita na gaggawa.

NEMA ta ce:

"Wasu marasa galihu sun koma matsuguni na wucin gadi, yayin da manya ke aikin ceto kayayyansu da ambaliyar ruwa ta shafa.
“Haka kuma, hukumar NEMA tana bayar da taimako ga wanda katangarsa ta ruguje, wanda sai an sake gina shi saboda daidaita tubalin ginin da hana shi rushewa, biyo bayan umarnin babban daraktan hukumar."

Kara karanta wannan

Da gaske sojoji sun kwace mulki a kasar Kongo? Mun binciko muku gaskiyar batu

Hukumar ta kuma tabbatar da cewar an tura kayan agaji kamar kayan yara, kayan mata, katipu, sabulai da sauran kayan amfani da za a rabawa mutanen da abun ya shafa.

Wata da ruwa ya shiga gidansu a yankin Arigbala da ke Orile Agege ta bayyana irin tashin hankalin da suka shiga.

Aisha Sani ta ce:

“Na ga tashin hankali domin maigidana ya yi tafiya a lokacin da ruwan sama ya shigar mana gida a ranar Asabar. Allah dai ya takaita abun bai yi mana barna ba sosai domin dai mun samu agaji daga wajen makwabta da suka taya mu kwashe ruwan.”

Ambaliyar ruwa a jihar Kebbi ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa akalla mutane uku ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta wakana a Dakingari da ke karamar hukumar Sulu ta jihar Kebbi.

Shugaban karamar hukumar Sulu Alhaji Muhammad Lawal Suru ne ya bayyana hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel