'Yan Bindiga Sun Mamaye Garuruwa 15 a Taraba, Sun Hana Manoma Girbi

'Yan Bindiga Sun Mamaye Garuruwa 15 a Taraba, Sun Hana Manoma Girbi

  • 'Yan bindiga sun tarwatsa garuruwan manoma 15 a jihar Taraba, sun raba mutane da amfanin gonakinsu a lokacin girbi
  • Wani mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan, Adamu Musa, ya ce 'yan bindigan suna kai masu hari dare da rana suna farautar mutane
  • Wani mazaunin Jalingi ya shaida wa Legit Hausa cewa yan bindiga sun hana jama'a sakat a ƙauyuka, yayansa na da gona amma ba ya zuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Taraba - Wasu miyagun 'yan bindiga masu ɗumbin yawa sun mamaye garuruwan noma 15 a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta tattara rahoton cewa a halin da ake ciki 'yan bindigan sun hana manoma girbe amfanin da suka sha wahala suka noma a gonakinsu.

Yan bindiga sun hana mutane sakat a kauyuka 15 a Taraba.
'Yan Bindiga Sun Mamaye Garuruwa 15 a Taraba, Sun Hana Manoma Girbi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Garin Gima, Bantaguru, Shadussa, Garin Bose, Mailabari, Gamfurum, Garbatau, Nayinawa da dai sauransu a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Mummunan Ibtila'i Ya Laƙume Rayukan Mata 5 a Cikin Mota

Mazauna wadannan kauyukan sun yi gudun hijira kuma a yanzu sun samu mafaka ne a Garba-Chede da sauran wurare a karamar hukumar Bali ta jihar, sun baro amfanin gonakinsu da suka girma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bamu da ikon cire amfanin gona - Musa

Ɗaya daga cikin manoman da lamarin ya shafa mai suna Adamu Musa ya ce ‘yan bindigar sun tilasta musu barin yankunansu ba tare da sun girbe shinkafa, masara, dawa, doya da sauran kayan abincin da suka shuka ba.

Ya koka da cewa bayan sun kwashe watanni suna aiki, ba za su iya girbe amfanin gonakinsu ba saboda ayyukan ‘yan bindiga a ƙauyukansu.

Musa ya ƙara da cewa da yawan mutane da suka ƙunshi mata da ƙananan yara an yi garkuwa da su yayin da 'yan bindigan ke farautar jama'a dare da rana.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP

A cewarsa, 'yan bindigan sun tare a yankunan kuma suna yawan kai hare-haren garkuwa da mutane, lamarin da ya sa baki ɗaya zaman lafiya ya yi ƙaranci, Leadership ta rahoto.

Ya bukaci gwamnatin jihar Taraba ta dauki matakin gaggawa na tunkarar matsalar tsaro a yankunan da suka dogara da noma don manoma su samu sa'ida.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ya ce tuni jami'an tsaro suka dira yankunan domin tarwatsa 'yan ta'addan da suka hana zaman lafiya.

Ya ce sun fara aikin tsaro na hadin gwiwa da ya ƙunshi sojoji, ‘yan sanda, mafarauta da ’yan banga, duk a kokarin da suke na ganin an fatattaki masu aikata laifuka a yankunan da lamarin ya shafa.

Wani mazaunin Jalingo, babban birnin Taraba, Malam Umar ya shaida wa Legit Hausa cewa yayansa yana da wata gona a kauyen Sabon Birni amma ya gaza zuwa.

Kara karanta wannan

Jimami Yayin Da 'Yan Bindiga Su Ka Sace Fitaccen Malamin Addini Da Wasu Mutum 2 A Jihar Arewa

Mutumin ya tabbatar mana da cewa halin da mutanen ƙauyukan Garbatau, Garin Hamidu da sauransu ke ciki a 'yan kwanakin nan abun a tausaya musu ne.

"Wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun addabi mutane a ƙauyuka, idan sun shiga nan aka tura jami'an tsaro gobe su kai hari wani ƙauyen daban."
"Sun hana mutane zaman lafiya, suna garkuwa da mata da yara. Yayana yana da wata gona amma bai iya zuwa saboda halin da ake ciki, gaskiya ya kamata gwamnati ta tashi tsaye."

Ginin Bene Mai Hawa 20 da Ake Gina Wa Ya Ruguje Kan Jama'a a Delta

A wani rahoton kun ji cewa Wani ginin bene mai hawa 20 da ake aikin ginawa ya ruguje a Asaba, babban birnin jihar Delta.

A cewar wani ganau da ibtila'in ya auku a kan idonsa, lamarin ya yi sanadin raunata mutane kusan takwas ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262